2023: Rikicin PDP Ba Zai Hanata Cin Zabe Ba – Okowa

Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP Ifeanyi Okowa ya gwasale gwamnan Ribas Nysome Wike da gwamnonin 4 da ke adawa da zamansa ɗan takarar mataimakin shugaban kasa cewa ta Allah ba ta su ba.

Okowa ya ce ” Muna so su dawo ayi tafiya tare amma idan suka kafe cewa ba za su yi mu ba to su kara gaba, ta Allah ba tasu, wannan karon PDP ce za ta yi nasara a zaɓen shugaban kasa ko suna so ka basu so.

” Abu ne kowa ya sani cewa ɗan takarar Shugaban kasa na APC bai cancanta, haka kuma na Labour shima dai tarkace ne, ba zai ci zaɓe ba. PDPn ne dai za ta yi nasara saboda haka mu ba ta su muke ba ta mutane muke yadda za mu karkato da hankulansu su gane haka su zaɓi PDP.

” APC ta yi watsawatsa da Najeriya. Idan muka yi nasara, za mu canja fasalin Najeriya gaba ɗayanta, za mu fasa ƙasar jihohi za su samu iko fiye da Abuja, sannan za mu kirkiro da ƴan sandan jihohi domin tabbatar da tsaro a sassan ƙasar nan.

” Mun zagaya kasar nan kaf ɗin kuma mun ji sannan mun gani, ƴan Najeriya yanzu gabaɗayan su sun gaji da yaudarar APC, kuma za su kai ta ruwa.

Labarai Makamanta