2023: Rikicin Cikin Gida Na Neman Zama Tarnaki Ga Manyan Jam’iyyu

A yayin da yaƙin neman zaɓukan 2023 na ke ƙaratowa, rikici yana ci gaba da dabaibaye manyan jam’iyyun siyasar ƙasar na APC da PDP.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya sha alwashin APC ba ta kai labari ba saboda batun ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa duk Musulmai ne, a ganinsa mummunan shiri ne na raba kan arewacin ƙasar.

Ya ce ba shi da tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ba ne kawai suke adawa da wannan tikiti na Musulmi da Musulmi na APC a kasar ba dukkanin Kiristoci musamman na Arewa na adawa da hakan.

A nasa ɓangaren, Yakubu Dogara ya ce batun tikitin Musulmi da Musulmi abu ne da ba zai haifar wa APC alheri ba, Dogara ya bayyana ra’ayinsa ne a Abuja ranar Larabar yayin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taron da gamayyar Kiristocin Najeriya ta shirya.

A ɓangaren Jam’iyyar PDP a ranar Laraba ne Gwamna Nyesom Wike da tawagarsa suka janye daga kwamitin yaƙin neman zaɓe na PDP saboda ƙin murabus ɗin da shugaban jam’iyyar ya yi.

Gwamnan da tawagarsa sun ce dole ne jam’iyyar ta miƙa shugabancinta ga ɗan yankin kudunci tun da ɗan arewa ne ya samu takarar shugaban ƙasa a PDP ɗin.

Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa kuma ɗan jarida a birnin Fatakwal na jihar Rivers, Lekan Ige, ya shaida wa sashen BBC Pidgin cewa masu adawa da tikitin Musulmi da Musulmi din nan a ganinsa ba don sun ƙi jinin jam’iyyar suke yi ba, suna yi ne don kare muradun mutane masu mabambantan ra’ayoyi.

Ya ce ya rage wa jam’iyyar APC ta warware matsalolinta kuma yana da tabbacin za ta yi hakan gabanin zaɓen da ke tafe.

Ya ce a zaɓen 1993 Najeriya ba ta damu da bambancin addini ba a lokacin da aka zaɓi ɗan takarar jam’iyyar SDP Moshood Abiola da mataimakinsa Babagana Kingibe, duk da cewa dukkansu Musulmai ne.

“Jam’iyyar ta koyi wani abu ne daga wancan yanayi kuma tana duba yadda za ta iya ɗinke ɓarakar da take da ita a yanzu,” in ji Ige.

Ige ya ce an ɗan tayar da jijiyoyin wuya a lokacin da Abiola ya zaɓi Kingibe a matsayin mataimakinsa amma ƴan jam’iyyar ne suka yi aiki tare don samar da ƴan takarar.

Ya ce ita kuwa PDP, ya rage nata ta tsara dabarun warware matsalolin da take fama da su. Ige ya ce wannan duk siyasa ce, kuma jam’iyyar za ta yi ƙoƙarin warware rikicin idan dai har suna son yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ya ce daga yanzu zuwa watan Fabrairu lokaci mai dan tsawo kuma komai na iya faruwa, wanda a ƙarshe za su iya fitowa su ce matsalar cikin gida ce kuma an sasanta.

“Idan ba su warware matsalar ba kuma, za su kawo tarnaƙi ga damarmakin jam’iyyun wajen cin zaɓukan shekarar 2023,”

2- Ambaliyar Ruwa Na Neman Shafe Birnin Legas

Yayin da mazauna Legas da ke ci gaba da fuskantar matsalar ambaliyar ruwa kowacce shekara, musamman a watannin Maris zuwa Nuwamba, a ‘yan shekarun nan yankin na fama da mummunan matsalar ambaliyar ruwa.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da hukumomi a Najeriya ke ci gaba da gargadin aukuwar wata ambaliyar nan da dan lokaci kadan.

Haka zalika masana na ganin cewa birnin na Legas ya fara nutsewa a cikin ruwa, sakamakon matsalar dumamar yanayi.

Tuni gwamnatin Jihar ta sanar da jama’a musamman waɗanda ke maƙwabtaka da bakin ruwa da su yi gaggawar kauracewa yankin domin kaucewa afkawa cikin Iftila’in.

A hannu guda kuma birnin Haɗeja na jihar Jigawa shima yana cikin mawuyacin hali sakamakon matsalar Ambaliyar ruwa da ta addabi yankin, inda jama’ar cikin birnin ke cikin damuwa da tashin hankali gami da fargaba na abin da zai je ya dawo.

Hakazalika wannan Iftila’i na ambaliyar ruwa ya yi ta’adi a Jihar Neja inda ruwan ya lashe maƙabartu da tafiya da tarin gawarwaki a cikin makon da ya gabata a yankin Mariga dake Jihar.

Jihohin Najeriya da dama na fuskantar barazanar faruwar Iftila’in ambaliyar ruwa kamar yadda masana suka faɗi na cewar an jima ba a ga irin wannan Iftila’in a faɗin ƙasar ba a tsawon shekaru.

Labarai Makamanta