2023: Najeriya Za Ta Rushe Idan Aka Yi Zaben Tumun Dare – Obasanjo

Rahotannin dake shigo mana daga Ikko babban birnin Jihar Legas na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Laraba ya buƙaci ƴan Najeriya da su tabbatar sun zaɓi shugabanni na gari a zaɓukan 2023.

Ya yi gargaɗin cewa idan har aka yi zaɓen tumun dare to ƙasar na iya rushewa.

Obasanjo ya yi wannan magana ne a matsayinsa na babban baƙo a wajen wani taro da aka yi a Lagos.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa yana fatan idan har aka zaɓi shugabannin da suka dace a 2023, to ƙasar za ta ga ci gaba mai yawa.

“Idan har muka zaɓi shugabanni na gari a 2023 to tabbas za mu kai ga ci.”

“Amma idan muka yi zaɓen tumun dare to lallai za mu dilmiye,” a cewar Obasanjo.

Tun da fari sai da Obasanjo ya yi bayanin cewa ƙasar ba ta ɗaukar matakan da suka kamata wajen yaƙi da talauci da rashin tsaro.

Labarai Makamanta

Leave a Reply