A daidai lokacin da babban zaɓen shekarar 2023 ke ƙara gabatowa, gamayyar kungiyoyin matasan Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga ɗan takarar jam’iyyar Action Alliance Manjo Hamza Al-Mustafa a takarar shugabancin ƙasa.
Shugaban Kungiyar Matasan Najeriya Alhaji Abdullahi Abubakar Wali ya bada wannan tabbaci a yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a garin Kaduna.
Matasan sun bayyana Hamza Al-Mustafa a matsayin jajirtacce wanda ya cika dukkanin sharuddan zama shugaba kuma ya ke gaba da dukkanin ‘yan takarar shugabancin kasar gaba dayansu.
“La’akari da irin kyakkyawan tarihin da Hamza Al-Mustafa ke dashi a lokacin da yake matsayin babban mai tsaron marigayi tsohon shugaban ƙasa Sani Abacha, da irin namijin kokari da gudunmawa da ya bayar wajen ciyar da Najeriya gaba ya sanya kafatanin matasan Najeriya Arewaci da kudanci yin mubaya’a ga takarar tashi”.
Matasan Najeriyar sun kuma yi tsokaci dangane da zama da ‘yan takarar shugabancin kasa da kungiyoyin Arewacin Najeriya ke yi a Kaduna, inda suka bayyana hakan a matsayin abin da ya dace amma duk da haka ya kamata su faɗaɗa ganawar tasu ga dukkanin ‘yan takara domin kauce dukkanin wani zargi ko hasashe mara kyau da za a iya yi musu.
Daga ƙarshe Matasan Najeriyan sun yi kira ga dukkanin ‘yan Najeriya da su goyi bayan takarar Shugabancin ƙasa na Hamza Al-Mustafa, domin a cewar su shine wanda ya fi cancanta akan dukkanin ‘yan takara, a matsayinsa na matashi jajirtacce wanda babu cin amana a tarihin sa, wanda zai kai Najeriya ga tudun mun tsira.
You must log in to post a comment.