Dan takarar zama gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana farin cikin sa ganin yadda mata su ka nuna masa ƙauna da goyon baya a kan takarar sa.
Sanatan ya yi godiya ga Allah da ganin irin cincirindon da mata su ka yi don nuna goyon bayan su gare shi.
Uba Sani ya ce, “Alhamdu lillah. Hakika mata su ne kashin bayan dukkannin al’umma, kuma kowa ya sa da cewa mata su ke bada kuri’a a ranar zabe. Don haka, kamar yadda ku ka fito a yau, ku fito a ranar zabuka, ku zabi jam’iyyar APC tun daga sama har kasa, kuma ku bi ‘yan’uwan ku mata gida gida, ku fada masu su zabi APC don ci-gaban ku da na ‘ya’yan ku”
Uba Sani ya ce, “In Allah ya yarda za mu rike maku amana. Kuma ci-gaba da ku ka gani a Jihar Kaduna, wanda shugaban mu ya kawo Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i, ba za mu ba ku kunya ba da yardar Allah. Za mu dora Kaduna na mata ne da yardar Allah.”
Haka kuma ya yi godiya ga dukkan matan jihar Kaduna da su ka fito dubunnan su, su ka nuna goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ni kai na da kuma dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC, ta bagaren hadin kai na tattaki, wanda matar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Isma El-Rufa’i ta jagoranta.
Dan takaran ya ci-gaba da cewa, “Ayyuka za su ci-gaba ta hanyar saka mata a cikin siyasa da gwamnati, kamar yadda da ma Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya assasa.”
Sannan ya yi godiya ga Mamman Lagos Support Group (MLSG) da The Women In Politics (W.I.P), bangare Kaduna na saka wa taron karsashi tare.
An dai yi wannan taro ne na tattaki a dandalin Murtala Square da ke Kaduna, wanda Ƙungiyar Mamman Support Group (MLSG) da Ƙungiyar The Women In Politucs (W.I.P), karkashin jagorancin uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Isma El-Rufa’i.
You must log in to post a comment.