2023: Magoya Bayan Atiku Sun Bukaci Ya Hakura Dalilin Tsufa

Gamayyar kungiyoyin masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun shawarci Wazirin na Adamawa ya hakura da yin takarar shugaban kasa a 2023 amma ya goyi bayan dan takara daga kudu maso gabashin kasar.

Kungiyoyin sun hada da Middle Belt Network for Atiku, North For North Support Group for Atiku, Turaki Arewa Vanguard for Atiku da South-West Development Frontiers.

Kawo yanzu Atiku bai riga ya bayyana cewa zai fito takarar shugaban kasar ba a hukumance amma ana hasashen yana shirin sake neman kujerar shugaban kasar.

A jawabin da ya yi yayin taron manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, Femi Osabinu, shugaban South-West Development Frontiers, ya ce shekaru sun fara yi wa tsohon shugaban kasar yawa wanda ya zama wajibi ya ja da baya.

An ruwaito cewa Osabinu ya ce Najeriya na bukatar matasahi mai jini a jika da zai iya jure ayyukan da ake bukata shugaban kasa ya yi. “Muna kira ga tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya sake shawara game da niyyarsa na sake yin takarar shugaban kasa a 2023. “Duk da cewa mun san Atiku ya hidimtawa kasa sosai, hakan yasa muka goyi bayansa tsawon shekaru, amma kuma bai dace mai shekaru 77 ya shiga takarar ba duba da irin kallubalen da kasar ke fama da shi.

“Najeriya na bukatar matashi mai ji da karfi wanda zai hada kan kasa ya kuma iya jure wa yawan ayyukan da ke tattare da zama shugaban kasa ya kuma samar da mafita ga matsalolin Najeriya.” Ya kara da cewa mambobinsu a sassan kasar nan a wasu jam’iyyun suna tuntubar wadanda suka dace domin ganin an zabi shugaban kasa dan kudu a 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply