2023: Kwankwaso Ya Samu Abokin Tarayya A NNPP

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Masanin harkokin masana’antu, Olufemi Ajadi, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP.

Ajadi, shugaban masana’antar haɗa kayan sha, Bullion Neat Global, ya bayyana aniyarsa a Sakatariyar NNPP ta ƙasa dake Abuja ranar Alhamis.

Yayin da yake ayyana tsayawa takarar shugabancin kasar Ajadi, ya yi alƙawari samar da tsayayyun ofisoshin siyasa a ƙasar nan.

“Wannan ce jam’iyya ɗaya tilo da take da manufa da irin wacce muke ta yawon nema, ita ce jam’iyyar da ta tara matasan Najeriya waɗanda nake wakilta, da kuma sauran yan Najeriya.”

“NNPP ce kaɗai jam’iyyar da zata share mana fage da kowane ɗan Najeriya daga kowane sashi zai sha romon demokaraɗiyya.” “Saboda haka, ina kira ga matasan Najeriya su shirya su ɗaura ɗamara, lokaci ya yi da zamu kawo canjin da muke fatan gani a ƙasar mu.”

Ajadi ya yi amfani da wannan dama wajen kira da nuna ladabi ga abokan takararsa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sunday Oginni wanda ke neman takarar gwamna.

Labarai Makamanta

Leave a Reply