2023: Kuyi Watsi Da Batun Addini Da Kabila Ku Zabi Cancanta – Sanusi

Khalifan Tijjaniyya na Najeriya Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci wadanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a su je su yanki katin zaɓe gabanin babban zaben 2023.

Yana magana ne a wajen taron shekara-shekara na tunawa da ranar haihuwar mazon Allah Annabi Muhammad SAW a garin Lokoja.

Sanusi ya yi kira ga jama’a idan zaɓen ya zo su zaɓi shugabanni na gari ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba.

“Idan matasanmu suka samu aikin yi, tattalin arzikin kasar baki daya zai inganta. Mafi mahimmanci, mu ba jam’iyya ba ce, amma ba za mu iya naɗe hannayenmu mu yi watsi da siyasa ba” in ji shi.

“Duk dan Tijjaniyya daga shekara 18 zuwa sama namiji ko mace je ka karbi katin zabe. Allah yana umurce ku da ku dogara ga hannun muminai amintattu.

Yanzu muna wani lokaci da jama’a ne ke da ikon naɗa shugabanni, ƙuri’arku ita ce ƙarfin ku, kuna da nauyi a kanku’’ a cewar Muhammadu Sanusi II.

Labarai Makamanta