2023: Kungiyar Inyamurai Ta Goyi Bayan Takarar Peter Obi

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide, kungiyar yan Inyamurai ta Duniya, ta jadada goyon bayanta ga Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben dake tafe na 2023:

Rahotanni sun bayyana cewar Kungiyar tana da banbanci da Ohanaeze Ndigbo, karkashin jagorancin George Obiozor.

Emmanuel Iwuanyanwu, shugaban, dattawa na Ohanaeze, ya ce kungiyar ta yi imanin cewa goyon bayan Obi ne abin da ya dace, kuma mafita ga al’ummar Inyamurai.

Da ya ke magana a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, a karshen taron kwamitin kudi da cigaba na kungiyar, Iwuanyanwu ya ce gamayyar ta kunshi shugabanni daga kudu maso gabas, kudu maso kudu da yankin tsakiya don goyon bayan Obi a babban zaben 2023.

“Wasu da dama cikinsu har yanzu suna ganin lokaci ne na Igbo, kuma a hikimarsu, sun ce shugabancin kasa ya koma yankin kudu maso gabas. “Sun cimma matsaya guda na goyon bayan Peter Obi, tabbas, mu Igbo a Ohanaeze muna farin ciki.

“Gaskiya shine Ohanaeze Ndigbo Worldwide na cikin wadanda suka amince kudanci da yankin tsakiya su goyi bayan takarar Peter Obi.”

Labarai Makamanta