2023: Ka Da Kuyi Gangancin Zabar Musulmai A Shugabancin Kasa – Dogara Ga Kiristoci

Tsohon shugaban majalisar Tarayya Yakubu Dogara ya gargaɗi Kiristocin Najeriya kada su barnata kuri’un su wajen zaɓen jam’iyyar APC, da ta tsaida musulmi ɗan takara, musulmi mataimaki.

Idan ba a manta ba tun bayan sanar da Kashim Shettima ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC da Tinubu yayi Yakubu Dogara, Lawal Babachir da Sanata Elisha Abbo wanda duk ƴan Arewa ne suka fito karara suka soki abin.

Bayan haka sun yi kira ga duka kiristocin Najeriya kada su zaɓi jam’iyyar APC domin ta tsayar da duka ƴan takaran ta musulmai.

A wurin taron majalisar kiristoci ta Najeriya da aka yi wanda Dogara ya halarta kuma yayi jawabi ya ce ” Ina kira ga kiristocin Najeriya kaf ɗin su kada su barnata ƙuri’un su wajen zaɓen jam’iyyar APC da suka tsaida Muslim-Muslim, domin Najeriya ba na musulmai bane kawai. Lallai Kiristoci su ƙaurace wa APC domin addinin mu ya yi hani da barnata abu.

” Mun gargaɗi APC kada su yi wannan ganganci na Muslim-Muslim amma suka yi mana kunnen uwar shegu suka tsaida musulmai biyu. Muna tabbatar muku mu kiristocin kasar nan za mu nuna musu ba su isa ba. Saboda haka kada wani kirista ya zaɓi APC domin barnar kuri’an sa kawai zai yi.

Dogara ya kara da cewa ” A kwai manyan malamn musulunci da suka ga rashin dacewar wannan tafiya kuma sun yi suka da hakan. Kun ga ashe ba mu kadai bane muke adawa da wannan ganganci har da musulmai.

Labarai Makamanta