2023: Ka Da Ku Zabi ‘Yan Romon Baka – Gargadin Sanusi Ga ‘Yan Najeriya

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya gargaɗi ‘yan jama’a cewa gyaran Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, yana mai cewa duk ɗan takarar da ya faɗi akasin haka “ƙarya yake yi”.

Kazalika Sanusi, wanda tsohon gwamnan babban bankin kasa ne ya shawarci masu jefa ƙuri’a da kar su zaɓi duk ɗan siyasar da ya ce gyaran Najeriya abu ne mai sauƙi.

“Matakan da za a ɗauka na gyara wannan [Najeriya] ba za su yi daɗi ba,” in ji shi yayin da yake magana a taron zuba jari da gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya ranar Asabar.

Taron ya samu halartar manyan baƙi kamar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu da sauransu.

Haka nan, Ƙaramar Ministar Kasuwanci Mariam Yalwaji Katagum ce ta wakilci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wurin taron da ake kira KadInvest, wanda ake gudanarwa shekara-shekara karo na bakwai – 7.0.

Labarai Makamanta