2023: Jihar Zamfara Ta Tinubu Ce – Tsohon Gwamna Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari ya ce, masu kada kuri’u a jihar a shirye suke su zabi dan dan takarar shugaban kasan APC, Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023 mai zuwa. Yari ya kuma bayyana cewa, mutan Zamfara a shirye suke su sake ba gwamna Bello Matawalle kuri’unsu a zaben na 2023.

Yari ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a karamar hukumar Talata Mafara a yayin wani katafaren kamfen na sanatan Zamfara ta Yamma a yankin.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, tawagar kamfen ɗin Yari ne ya shirya gangamin karkashin shugabancin tsohon shugaban APC na jihar, Alhaji Lawal Liman.

“Sakamakon yakin neman zaben APC na yau a Talatar Mafara ya nuna cewa mutanen Zamfara suna goyon bayan APC dari bisa dari. “Dukkan ‘yan Najeriya ya kamata su zabi APC a kowacce kujera don kawo ayyukan ci gaba masu ma’ana a kowane mataki.” A cewarsa, Tinubu da Matawalle na da shirin ayyuka masu kyau ga ‘yan Najeriya da mutanen Zamfara, wadanda za su ciyar da al’umma gaba.

Yari ya kuma yabawa wadanda suka shirya gangamin kamfen din, tare da bayyana jin dadinsa da ganin irin wannan karimci da nuna goyon baya da suka yi. Ya kuma danganta sulhunsa da gwamna Matawalle da sauran masu ruwa da tsaki na APC da tushen nasarar APC a zabe mai zuwa.

Labarai Makamanta