2023: Jama’ar Karamar Hukumar Sanga Sun Yi Mubaya’a Ga Sanata Uba Sani

Sakon Sanata Uba Ga Alummar Sanga: Ku Zabi APC Daga Sama Har Kasa

Dan takarar gwaman jihar Kaduna a jamiyyar APC Sanata Uba Sani ya bukaci masu jefa kuri’a a jihar da su zabi jam’iyyar APC daga sama har kasa.

Sanata Uba Sani ya kara da cewa, yana da tabbacin cewa, yan takarar jam’iyyar APC ne zasu inganta rayuwar Al’umma.

Uba Sani ya yi wannan kiran ne a garin Gwantu da ke karamar hukumar Sanga a lokacin da ya gana da al’ummar yankin.

Dan takarar wanda yake kan zagaye na bakwai na yakin neman zabensa ya ce, daukcin ‘yan takarar APC an gwada su an kuma aminta da su.

Ya ce, ku tabbatar da kun zabi wadanda kuka san za su samar maku da romon dimokiradiyya.

Ya ci gaba da cewa, ya gabatar da kudurori 32 a gaban majalisar dattawa ya kuma giggina asibitoci da makarantu a karamar hukumar wacce ta ke a cikin mazabarsa.

Uba ya yi alkawarin cewa, zai dinga tuntubar jama’a da kuma masu ruwa da tsaki a jihar wajen wanzar da tsare-tsare da shirye-shirye in Allah ya ba shi nasara ya zamo gwamnan jihar a 2023.

Sanata Uba ya yi nuni da cewa, fatara ba bu ruwanta da maganar kabilanci ko addini, inda ya ce, zamu mayar da hankali wajen kirkiro da sana’oin hannu ga mata da matasa na jihar tare da ba su tallafin kudade don yin sana’oin, mussaman don su zamo masu dogaro da kansu.

A na sa jawabin Dagacin Fadan Ninzo, Ibrahim Mamman a madadin sauran masu rike da sarautar gargajiya a yankin sun mika godiyar su ga gwaman jihar Mal Nasir El-rufai bisa samar masu da tsaro da kuma inganta fannonin ilimi da lafiya.

Basaraken ya kuma roki Sanata Uba in ya samu zama gwamnan ya kara yawan albashin da gina masu anguwannin da ke a kauyuka da gina masu matsugunnai masu kyau.

Labarai Makamanta