2023: Ina Goyon Bayan Mulki Ya Koma Kudu – Ganduje

Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce yana goyon bayan Shugabanci ƙasar nan ya koma kudanci a zaɓen Shekarar 2023 da ke tafe domin cigaba da samun nasarar ɗorewar mulkin dimukuraɗiyya a Najeriya.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin hirar da aka yi da shi a cikin shirin Politics Today na gidan Talabijin naChannels ranar Juma’a.

“Kudancin Nijeriya ya dace a ba takara amma ya kamata a samu hadin kai tsakaninsu,” domin muddin babu fahimta da haɗin kai abubuwa ba za suyi daidai ba”.

“Karba-karba duk da cewa bata cikin kundin tsarin mulkin tarayyar Nigeria tsari ne na cin zabe, kuma yana taimakawa wajen karin samun haɗin kai da haɓakar siyasar Najeriya.

Da aka masa tambaya shin ko APC ta tabuka abin a zo a gani tun bayan lashe zabe da ta yi a 2015, ya amsa da cewa eh. Ya ce jam’iyyar APC a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ta inganta tsaro sannan tana gyara tattalin arzikin kasar.

Ganduje ya ce yana kyautata zaton jam’iyyar mai mulki za ta yi nasara a babban zaben 2023 da ke tafe ta cigaba da jagorancin ƙasar. Amma ya ce akwai bukatar jam’iyyar ta yi shiri mai kyau tare da bincike kan hanyoyin da suka fi dacewa domin sake cin zabe a kasar.

Labarai Makamanta