Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi alkawarin samar da kayayyakin da ake bukata na goyon baya ga dan takarar shugaban Ć™asa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da Kwankwaso ya kai ziyara Jihar Ribas don kaddamar da wasu ayyukan tituna da Gwamna Wike ya yi a jihar.
Wike, wanda jigo ne na jam’iyyar PDP ya gayyaci Kwankwaso domin kaddamar da ayyukan da ya yi, inda ya siffanta dan takarar na NNPP mai nagarta da Najeriya ke bukata.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, ya nemi Kwankwaso kada ya bar PDP a watan Maris, amma makiyan cikin gida a jam’iyyar suka tursasa shi barinta. Wike ya ce Kwankwaso ne zai iya hada kan Najeriya wuri guda, amma kash, ba a jam’iyya daya suke a a yanzu ba.
You must log in to post a comment.