2023: Duk Wanda Zai Yi Takara Ya Aje Aiki – Buhari Ga Ministoci

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci ministocinsa masu son takara su yi murabus daga nan zuwa 16 ga watan Mayu.

Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed ne ya sanar wa da manema labarai hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa na mako-mako a ranar Laraba da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Tun da fari a ranar 25 ga watan Fabrairun 2022 Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan majalisa tarayyar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri’a a zaben shugabannin jam’iyya ko kuma na ‘yan takara.

Shugaban ya nemi hakan ne a lokacin da ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta kasar wadda aka dauki tsawon lokaci ana ka-ce-na-ce a kanta.

Sai dai ‘yan majalisar dokokin ƙasar sun yi watsi da buƙatar Shugaba Buhari na cire wani sashe daga sabuwar dokar zaɓe, inda tun a lokacin alamu suka nuna cewa wasu daga cikin ƙusoshin gwamnatin tarayya da na jihohi na cikin ruɗani.

Dukkanin zaurukan majalisun tarayyar biyu – ta wakilai da ta dattawa – sun ƙi amincewa da gagarumin rinjaye su gyara sashe na 84(12) da ya tanadi cewa wajibi ne masu riƙe da muƙaman siyasa su ajiye aikinsu kafin su iya jefa ƙuri’a a zaɓen jam’iyyu ko kuma a zaɓe su.

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci Buhari, da Babban Lauyan gwmnatin tarayya kuma Ministan Shari’a (Antoni Janar), Abubakar Malami, da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan kar su sauya sashen dokar.

Da yake bayar da umarnin a ƙarar da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta shigar, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ce dokar zaɓen ta zama cikakkiyar doka kuma ba za a iya sauya ta ba tare da bin tsarin doka ba. Sai dai Ahmad Lawan ya ce kotun ba za ta hana su yin aikinsu na majalisa ba.

Jerin ministocin da wannan umarni zai iya shafa:

Chibuike Rotimi Amaechi – Ministan sufuri

Godswill Akpabio – Ministan harkokin Neja Delta

Ogbonnaya Onu – Ministan kimiyya da fasaha

Chris Ngige – Ministan ƙwadago

Emeka Nwajiuba – Ƙaramin ministan ilimi

Timipre Sylva – Ƙaramin ministan albarkatun man fetur

Abubakar Malami – Ministan Shari’a

Paulline Tallen – Ministar harkokin mata

Akwai yiwuwar wannan umarnin zai yi tasiri ga yanayin gudanar da gwamnati sakamakon adadi mai yawa da wannan umarnin na Shugaba Buhari zai iya shafa.

Sai dai mai magana da yawun shugaban ya ce wannan lamarin ba zai shafi harkokin gudanar da gwamnati ba.

Labarai Makamanta