Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki mutanen jihar Adamawa su zaɓi dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, da Aishatu Binani kujerun shugaban kasa da gwamnan jihar Adamawa.
Dubban magoya bayan jam’iyyar APC ne suka halarci wannnan gangami.
A jawabin da yayi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga mutanen jihar Adamawa su zaɓi Binani mace ta farko da za a zaɓa gwamna a kasar nan idan Allah ya yarda.
Jihar Adamawa dai ita ce jihar ɗan takarar shugaban kasa na PDP wato Atiku Abubakar, sannan kuma gwamnan dake kan mulki, Ahmadu Fintiri shima ɗan PDP ne.
Ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa ta jam’iyyar APC, Aisha Binani ta bayyana cewa abinda ya sa talakawa ke ƙaunarta a jihar Adamawa shine saboda kula da su da take yi.
Binani ta bayyana haka a lokacin da take amsa tambayar manema labarai a fadar shugaban kasa yayi kammala ganawa da shugaba Buhari da ta yi.
Binani ta ce ta ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne don ta gode masa bisa amsa gayyatar da yayi na halartar gangamin kaddamar da kamfen din ta na gwamna.
You must log in to post a comment.