Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

2023: Buhari Ya Kalubalanci Jami’an Tsaro Da Zama ‘Yan Ba Ruwanmu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga hukumomin tsaron ƙasar da za su yi aiki da hukumar zaɓen ƙasar a lokacin zaɓukan 2023 da ke tafe da su kasance ‘yan ba-ruwanmu, tare da nuna ƙwarewar aiki.

Sannan kuma su nesanta kansu daga duk abubuwan da za su kawo matsala ga ayyukansu.

Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga jami’an ne ranar Laraba a lokacin bikin ƙaddamar da rukunin gidajen jami’an hukumar tattara bayanan sirri a unguwar Idu da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Buhari ya umarci hukumomin tsaron da su tabbatar da cewa sun kula da ayyukan rarraba tare da lura da muhimman kayayyakin zaɓe cikin nuna ƙwarewar aiki kamar yadda yake kunshe cikin dokokin hukumomin tsaron.

Exit mobile version