Burtaniya ta ce ta zura ido kan ‘yan siyasa da jam’iyyunsu, jami’an tsaro da duk wani mutum da zai haifar ko ingiza rikici ta shafuka sada zumunta gabannin babban zaɓe da ke tafe a 2023 a Najeriya.
Jakadiyar Burtaniya a Najeriya, Catriona Laing ce ta sanar da hakan lokacin ganawa da kwamitin gudanarwa ta harkokin zaɓe na PDP a Abuja.
Ms Laing ta ce zaɓen 2023 na da muhimmanci sosai ga Afirka da duniya baki ɗaya, don haka dole ido na kan Najeriya kuma Burtaniya za ta zura ido sosai a kan ƙasar.
You must log in to post a comment.