2023: Biliyan 100 Da Aka Ware Ba Zai Isa Ba – Hukumar Zabe

Labarin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce naira biliyan 100 da aka ware domin gudanar da babban zaben 2023 a kasafin kudin shekara mai zuwa ba zai isa ba ko kadan.

Yakubu ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 5 ga watan Nuwamba, lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan zaɓe domin kare kasafin kudin hukumar na 2022.

Ya ce yayin da aka warewa babban zaben 2019 naira biliyan 189, babu ta yadda za a yi na 2023 ya zama naira biliyan 100 kawai, ya zama wajibi kwamitin ya yi duba akan haka.

Mahmood ya ce naira biliyan 100 kason farko ne na zaben 2023 yayin da naira biliyan 40 ya kasance kasafin kudin shekara na hukumar.

“Tuni muka fara tattaunawa da ma’aikatar kudi ta tarayya kan karin bukatu don zaben 2023. “Imma mu zo majalisar dokokin tarayya domin kare kasafin kudin a gaban kwamtin ko kuma za mu yi abun da muka yi a 2019 lokacin da bangaren zartarwa ya gabatar da kudirin ga majalisar kasa kawai mu kuma muka zo don kare shi.

“Za mu bukaci karin kudi saboda mun fadada rumfunan zabe kuma za mu gabatar da sabbin fasahohi don zabe da sauransu. Adadin masu zabe da aka yi wa rajista za su karu fiye da miliyan 84 na babban zaben 2019.”

Da yake bayar da rabe-raben yadda ake son kashe kudin don zabe mai zuwa, shugaban na INEC ya ce hukumar ta ware naira biliyan 7.3 don siyan kayayyaki. Ya ci gaba da cewa: “Mun kuma ware naira biliyan 7 don gudanar da zabukan gwamnan Ekiti da Osun.

“Mun yi tanadin naira biliyan 2.6 ga Jihar Ekiti mai yawan mutane sama da miliyan daya da suka yi rajista da kuma naira biliyan 4.4 ga Osun mai kananan hukumomi 30. “Za mu ware naira biliyan 4.2 don ci gaba da yin rajista a cibiyoyi 2,700 da kuma naira miliyan 619 don sa ido kan taron jam’iyyu da ayyukan yakin neman zabe.

“Ba ni da tabbacin zai isa. Muna sa ido kan tarukan jam’iyyu da zabukan fidda gwani tun daga matakin unguwanni ta hanyar wakilai. Muna da gundumomi 8,809 da jam’iyyun siyasa 18.

Labarai Makamanta