Tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya karyata rahotannin da wasu kafafen sada zumunta suka wallafa cewar ya goyi bayan takarar Peter Obi, na jamâiyyar LP a zaben 2023.
Babangida ya karyata hakan ne ta hannun mai magana da yawunsa, Prince Kassim Afegbua, inda ya ce, mai gidansa Babangida bai fitar da wata sanarwa a kan goyon bayan takarar Peter Obi ba.
Kassim ya kara da cewa, tsohon shugaban kasar bai da wani shafi a Twitter ko wata kafar sadarwa ta zamani.
Ya bayyana cewa, wannan labarin na kanzon kurege ne, inda kuma ya yi kira ga âyan Nijeriya da su yi watsi da rahoton domin bai da wani tushe ballantana makama.
Ya sanar da cewa, idan har mai gidansa zai yi wata magana, yana fitar da sanarwa ne ba ta kafafen sada zumunta ba.
You must log in to post a comment.