2023: Bamu Da Zabin Da Ya Wuce Tinubu – El Rufa’i

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamna Nasir El-Rufai ya fito fili ya bayyana goyon bayan sa ga kudirin jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na takarar shugabancin kasa a 2023.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a dandalin Murtala da ke Kaduna inda Tinubu da tawagarsa da suka haɗa da tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, da tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribado da sauran manyan baki suka kai wa wakilai APC na jihar ziyarar neman goyon baya.

Gwamna El-Rufai ya ce zai bukaci goyon bayan wakilai daga jihar Kaduna domin marawa Tinubu baya a kokarin da yake na ɗarewa karagar shugabancin kasa a 2023.

“Ina so in yi wa Kashim Shettima gyara, saboda ya ce gwamnan yana tare da su,” ya kara da cewa ba zai iya zama cikakken masoyin Tinubu ba sai wakilan jihar sun amince.

“Kafin mu tabbatar da abin da Kashim Shetima ya fada a nan, ina so in tabbatar daga wakilan mu masu darajar cewa kuna tare da Asiwaju?” El-Rufai ya tambaya, wakilan suka amsa gaba daya suna ihun eh.

“Mai girma, ina yin abin da suka ce mini, su ne shugabannina. Haka APC a Kaduna ke aiki,” inji shi.

Labarai Makamanta