2023: Bai Zama Dole Jam’iyyar Labour Ta Dauki Kwankwaso Ba – Sakataren Jam’iyya

Babban Sakataren jam’iyyar Labour na Kasa Alhaji Umar Ibrahim Mai Raƙumi, yace a halin da ake ciki jam’iyyar ta mayar da hankali ne wajen zaɓo mataimaki da zai rufa wa ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Peter Obi baya daga yankin Arewacin kasar.

Mai Raƙumi ya ƙara da cewar babu shakka tattaunawa ta yi nisa tsakanin jam’iyyar da ɓangaren tsohon gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, amma hakan ba ya nuna cewar dole ne jam’iyyar sai ta ɗauki Kwankwaso mataimaki ba.

Babban Sakataren ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a garin Kaduna dangane da babban zaɓe na 2023 da ke tafe.

Umar mai Raƙumi ya cigaba da cewar Najeriya ta jima tana shan matsa a hannun tsofaffi daga manyan jam’iyyun nan biyu PDP da APC, amma a yanzu lokaci ya yi da ‘yan Najeriya ya kamata su canza taku, su zaɓi waɗanda suka dace domin ceto kasar daga rugujewa.

“Babban abin da ke jefa Najeriya cikin halin koma baya shi ne siyasar ɓangaranci, lokaci ya yi da za a yi watsi da wannan ɗabi’a a zaɓi cancanta ba tare da la’akari da yanki ƙabila ko addini ba”.

Labarai Makamanta