2023: Babu Matsala Idan Tinubu Ya Dauki Mataimaki Musulmi – Kayode

Tsohon Ministan Sufurin sama, Femi Fani-Kayode yace zai goyi bayan dan takaran shugaban kasan jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, koda ya zabi mataimaki Musulmi.

Kayode ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin ‘Politics Today’ na tashar ChannelsTV ranar Alhamis. Yace sam ba zai yiwu ace za’a cire addini daga cikin siyasa ba: “Matsala ne kuma wajibi ne mu yi wa mutane bayani idan muka yanke shawarar yin haka.

Ba ni da matsala idan aka yi haka (Musulmi da Musulmi). idan dan takarar mu Tinubu ya zabi hakan zamu goya masa baya.”

“Amma muna bukatar kare abinda muka zaba. Ba zai yiwu muce babu addini cikin siyasar yau ba. Musamman yanzu da aka kashe Kirista 50 a Coci a Owo kuma a Kaduna aka kashe Kirista 34.”

Cikin wadanda ake hasashen Tinubu zai zaba sune Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Kaduna, Nasir E-Rufa’i; Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje; Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Labarai Makamanta