Rahoton dake shigo mana daga garin Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewar Gwamnan jihar Abdullahi Sule, ya ce Allah ne kadai zai iya dakatar da Bola Ahmed Tinubu daga zama magajin shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaɓen dake tafe.
Gwamna Sule ya yi wannan furucin ne a wurin gangamin kaddamar da kamfen ɗin dan takarar Sanatan Nasarawa ta yamma a inuwar APC, Shehu Tukur, wanda ya gudana a karamar hukumar Kokona.
“Gwamnonin APC na arewa zasu zuba dukiyarsu domin tabbatar da Tinubu ya zama shugaban kasa, idan akwai masu kaunar Tinubu ya zama magajin Buhari a sahun farko to gwamnonin arewa ne.” “Allah ne kadai zai iya hana Tinubu da Abdullahi Sule zama shugaban kasa da gwamna.
Mun shirya zuba dukiyarmu da karfinmu damin mu binne duk wani hankoron yan adawa.” “Burinmu mu ga Tinubu, Sanatoci uku, mambobin majalisar wakilan tarayya biyar da mambobin majalisar dokokin jiha 24 sun zama zababbu a wata mai zuwa.”
Gwamna Sule ya musanta rahoton da ke cewa gwamnonin APC 11 na tattauna wa a boye da dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar. “Wannan karya ce tsagwaronta, gwamnonin arewa a APC ne suka matsa har Tinubu ya zama dan takara, zasu yi duk me yuwuwa su tabbatar ya zama shugaban kasa.”
You must log in to post a comment.