2023: Babu Ɗan Kudun Da Zai Iya Cin Zaɓe A Najeriya -Okorocha

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma Sanata mai wakiltar jihar Imo ta Yamma, Sanata Rochas Okorocha ya yi bayani akan cewa Inyamuri ba zai taba hawa shugaban kasar nan ba a 2023, sai dai idan dan arewa ya taimaka.

A wata tattaunawa da aka yi da Sanatan a Abuja, ya yi bayanin cewa Najeriya na bukatar shugaban kasa da zai tabbatar da tsaro, samar da aiyukan yi ga matasa tare da hada kan mutanen kasa.

Ya ce: “Kabilar Inyamurai kadai ba zasu taba iya shugabancin kasa ba, zai fi kyau idan suka koma ba wa ‘yan arewa da sauran yankunan kasar nan goyon baya, hakan zai sa su cimma burinsu.

“Nasan zamu zo wajen wata rana, lokacin da za ayi shugabanci kasa ba don addini ko kabila ba. Amma matukar muka cigaba da taimakawa kabilanci da banbancin addinai, ba zamu ga dai-dai ba.”

Okorocha ya jaddada cewa, kabilanci ko banbancin addinai bai kamata suna shiga siyasa ba, saboda talauci bai san kabila ko addini ba. “Saboda kabila ba zata ciyar da mutum ba kuma ba zata bada tsaro ba.”

“Kamar yadda kuka lura, siyasar kasar nan na hannun arewa ne saboda su ke da yawan kuri’u.

Wani abu mai nagarta da na sani game da arewa shine, musulmai ne. Musulmi nagari kuwa yana da kyan halin adalci da hadin kai. “Wannan kuwa shine burin da kowanne dan Najeriya na Kudu ke dashi.

Zata kuma iya yuwuwa, adalcin Arewa ta sa su amincewa dan Kudu ya shugabanci Najeriya,” ya kara da cewa.

Related posts