2023: Babangida Ya Goyi Bayan Osinbajo

Rahotanni daga Mina babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar tsohon shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya fi dacewa ya jagoranci Najeriya a 2023.

Babangida ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar bakuntar kungiyar ‘Osibanjo Grassroot Organisation’ a gidan sa dake garin Minna.

” Osinbajo mutum ne mai hakuri da hangen nesa sannan yana da tausayi da son hadin kai Najeriya. Hakan ya sa naga babu wani dan Najeriya da ya fi dacewa ya shugabanci kasar nan a 2023.

” Ni na san shi sani na hakika. Mutumin kirki ne kuma mutumin arziki ne mai son zaman lafiya. Najeriya kasace da ke bukatar shugaba nagari mai kishi da son hadin kai irin Osinbajo.

” Sako na gare shi shine ya ci gaba da kokari da dattaku kamar yadda ya ke yi a yanzu. Ina masa fatan Alkhairi.

Shugaban kungiyar Ojo Foluso, ya ce sun garzayo wajen tsohon shugaban kasar ne domin neman goyon bayan sa da kuma shaida masa burin so ga mataimakin shugaban kasa, Osinbajo.

Labarai Makamanta