2023: Ba Zan Sauya Ra’ayi Na Ba Lallai Mulki Ya Koma Kudu – El Rufa’i

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce babu gudu babu ja da baya a kan goyon bayan komawar shugabanci kasar nan a 2023 zuwa yankin kudancin Nijeriya.

El-Rufai ya ce yarjejeniyar ce aka yi, cewa bayan Muhammadu Buhari, shugabancin kasa zai koma kudu. Ya ce bai taba cewa ba zai goyi bayan ‘yan Arewa ko ‘yan Kudu ba, amma dole ne shugabanci ya koma kudu a 2023 duk da kuwa kundin tsarin mulkin APC bai gindaya hakan ba.

Kamar yadda ya ce, ko jam’iyyar PDP na da wannan yarjejeniyar ta karba-karba, wanda hakan ne ya sa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da marigayi Umaru Yar’adua suka yi mulki.

Labarai Makamanta