2023: Atiku Zai Riga Rana Faduwa – Kashim Shettima

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya ce ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da takwaran sa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, ba su da wani abin da za su iya ga yan Najeriya.

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba a Abuja, yayin wani taron kwana guda kan shirin da suka yiwa Najeriya.

Ya ƙara da cewar zaben shugaban kasa na 2023 zai zama Abin kwatance a tarihin Najeriya, yana mai cewa “Obi ba shi da wani abin da zai iya yi baya ga alkaluman da yake yawan furtawa na shaci-fadi.”

Shettima ya kuma ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ne zai kayar da Atiku da Obi, yana mai cewa Ya fi su tunani da basira.

Labarai Makamanta