2023: Atiku Ya Shawarci Matasan ‘Yan Siyasa

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sai da yayi takarar kujerar gwamna sau hudu kafin ya samu nasara daga karshe a shekarar 1999.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugabannin kungiyoyin magoya bayansa a birnin tarayya Abuja, Atiku yace yayi farin ciki matuka ganin matasa sun yi musharaka cikin siyasar kasa saboda babbar manufarsa itace horar da matasa don mika musu mulki.

“Ina farin cikin ganin matasa da yawa suna zuwa wajena suna ayyana niyyar takarar kujerun siyasa, wasu yan majalisar jiha, wasu majalisar dokokin taraya, wasu gwamna ma suke so.”

“Nima haka na fara. Na fara ina dan shekara 30. Lokacinmu yaki mukayi da mulkin Soja.” “A siyasa, kana bukatar mayar da hankali, jajircewa da zama mai manufa. Misali, na yi takarar gwamna sau hudu kafin aka zabeni daga karshe. Haka siyasa take.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply