2023: Atiku Ya Nada Tsoffin Janarorin Soji Kwamandojin Yakin Neman Zabe

A wani shiri mai kama da yaƙin a-yi-ta-ta-ƙare, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, ya naɗa tsoffin Janar-Janar uku na soja a cikin Rundunar Kamfen ɗin Cin Zaɓen Shugaban Ƙasa .

Aikin wannan Majalisar Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa shi ne ta shirya yadda za a yi yaƙin neman zaɓen 2023 na PDP.

Ana kallon babban zaɓen shekarar 2023 dake tafe a matsayin wani zaɓe da zai yi tasiri a Najeriya tun bayan sake ayyana Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a PDP da tikitin musulmi da musulmi da APC ta yi.

Labarai Makamanta