2023: APC Na Shirin Tafka Magudi A Kano – NNPP

Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta zargi jam’iyyar APC da shirya yadda zata rage yawan masu kada kuri’u a jihar ta hanyar yaudara tare da kwace katinan zaben jama’a.

Wannan ya faru ne a karo na farko a tarihin shugabancin jihar inda aka mayar da shugabanci zuwa gado kamar yadda NNPP tace sun bayyana a dokokin gwamnatin da nade-nadenta.

“Ɗan takarar da gwamna ya zaba” ya rantse da Qur’ani kan cewa zai cigaba da barnar da ake a jihar Kano ba tare da dakatar da ita ba.

Jam’iyyar ta yi wannan zargin ne a takardar da ta fitar bayan taron wayar da kai da ta hadawa ‘yan takarar gwamna, sanata, majalisar wakilai da majalisar jiha wanda aka yi a ranar 15 ga watan Satumban 2022 a Kano.

Takardar ta zargi gwamnan jihar da yin watsi da hakkokinsa na bai wa rayuka da kadarorin ‘yan jihar kariya. Kamar yadda takardar da aka saka hannu na hadin guiwa tsakanin shugaban horarwar, Garba Diso da sakatare, Hamisu Ali, sun yi kira da a hanzarta shawo kan barazanar tare da kira ga INEC da ta gaggauta wallafa sunayen wadanda basu karba katin zabe ba tare da wayar musu da kai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply