Hukuncin Rataye Abduljabbar Abin Farin Ciki Ne A Duniyar Musulunci – Dr. Mansur Sokoto Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan mazaunin Jihar Sokoto Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, ya bayyana hukuncin kisa da Kotu ta yanke wa Abduljabbar Nasiru Kabara a matsayin abin farin ciki a duniyar Musulmi gaba ɗaya. Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi fice wajen yin katoɓara a karatuttunkan sa musanman akan abin da ya shafi rayuwar Annabi Muhammad da Sahabbai. Lamarin da ya haifar da matsala a Jihar Kano har gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Ganduje ta shirya zaman muƙabala…

Cigaba Da Karantawa

Janye Tallafin Mai Shi Ne Mafita A Najeriya – El-Rufa’i

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi hasashen manyan matsalolin da sabon shugaban Najeriya zai fuskanta inda ya kama aiki, El-Rufai ya ce dole ne wanda zai karbi mulkin kasar nan ya yi kokarin shawo kan matsalar tattalin arziki. Gwamna Nasir El-Rufai ya ce don haka akwai bukatar a magance matsalar tallafin man fetur da kuma tashin da kudin kasar waje suke yi a halin yanzu. Gwamnan na Kaduna ya ce idan shugaban kasar da aka zaba ya yi…

Cigaba Da Karantawa

Zabena Ne Zai Share Wa Inyamurai Samun Zama Shugaban Kasa – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce shi tsani ne ga kabilar Igbo wajen fitar da shugaban kasar Najeriya daga cikinsu. Atiku, wanda ya yi magana a dandalin Alex Ekwueme, Akwa, a yayin taron gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Anambra, ya yi alkawarin taimakawa kabilar Igbo wajen fitar da shugaban kasa bayan wa’adinsa. “Zan zama matattakalar tabbatar da kabilar Igbo sun samu shugaban kasa muddin kuka zabe ni a 2023.” “Zaku iya tabbatar da hakan, in kun lura wannan…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Kotu Ta Tabbatar Da RiminGado A Halastaccen Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa

Kotun masana’antu ta kasa dake Abuja ta tabbatar da shugaban hukumar yaki da rasha ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji, wanda aka dakatar a matsayin Shugaban hukumar, Kotun ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta biya Magaji albashinsa da alawus din da ta rike masa bayan dakatar da shi a watan Yulin shekarar da ta gabata. An dakatar da shi na tsawon wata daya a watan Yulin 2021 bisa rashin amincewa amsar wani akawun hukuma daga ofishin akawu-janar na jihar. Kotun ta ayyana cewa har yanzu Magaji yana nan a…

Cigaba Da Karantawa

Shekaru Masu Albarka: Buhari Ya Cika Shekaru 80 A Duniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana mana cewar a Asabar ne 17 ga watan Disamban shekara ta 2022 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika shekara 80 da haihuwa. An haifi shugaba Buhari ne a ranar 17 ga watan Disamba a garin Daura na masarautar Daura da ke Jihar Katsina. Tuni manyan mutane Sarakuna, Malamai da ‘yan siyasa suka soma tura sakon taya murna ga shugaban kasar. Cikin wadanda suka soma aike sakon murnarsu ga shugaban akwai dan takarar shugabanci kasa a inuwar Jam’iyyar APC, Bola Ahmed…

Cigaba Da Karantawa