Buhari Abin Koyi Ne A Siyasar Afirka – Gwamnatin Amurka

Shugaban kasa Amurka Joe Biden ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa shayar da ‘yan Najeriya romon dimokradiyya da fadada dimokradiyar a nahiyar Afrika. Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu bayan ganawar Buhari da Biden a birnin Washington ranar Laraba. Idan baku manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Amurka don halartar wani taron shugabannnin kasashen Afrika a makon da ya gabata. Shugaban na Amurka ya ce, wannan taro Amurka…

Cigaba Da Karantawa

Nadin Ahmad Bamalli: Tsohon Wazirin Zazzau Ya Maka El-Rufa’i Kotu

Tsohon Wazirin masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu, ya maka Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, masarautar Zazzau da kuma wasu mutane 12 a gaban babbar kotun jihar. Aminu, ya maka su ne a gaban kotun a kan nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19. Aminu, wanda na daya daga cikin masu nada sarki a masarautar Zazzau, ya bukaci kotun ta soke martaba Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau. Da aka gabatar da karar a ranar Laraba wasu daga cikin wadanda Aminu ya maka a gaban…

Cigaba Da Karantawa

Mun Karbo Naira Biliyan 30 A Hannun Dakataccen Akanta Janar

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya ce zuwa yanzu an karbe N30bn daga hannun Idris Ahmed tsohon Akanta Janar na ƙasa. Wadannan biliyoyi su na cikin N109bn da ake zargin Idris Ahmed ya karkatar a lokacin yana rike da ofishin Akanta Janar na kasa. Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa ya shaidawa Duniya wannan a lokacin da ya halarci wani taro da aka yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Zan Sa Hannu Cikin Gaggawa Domin Rataye Abduljabbar – Ganduje

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Kwamishinan Shari’a na jihar yace gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace zai sa hannu kan hukuncin rataya da kotu ta yankewa Mallam Abduljabbar ba tare da ɓata wani lokaci ba. “Matsayar gwamna bai sauya ba kan sanya hannu akan hukunci da kotu ta yanke” 5 “Akwai matakan da ya kamata a bi kuma a shirye mai girma gwamna yake da zarar an kawo masa zai sanya hannu” “Babu wanda za a bari ya taka doka, kuma an dauki duk matakin da…

Cigaba Da Karantawa

Kalaman Batanci: Kotu Ta Yanke Wa Sheikh Abduljabbar Hukuncin Kisa

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad SAW. An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su. Mai Shari’a Sarki Yola ya ce malamin yana da kwana 30 don ɗaukaka ƙara idan bai gamsu da hukuncin ba. Cikin iƙirarin da Abduljabbar ya yi a wa’azizzikan da…

Cigaba Da Karantawa