Kano: Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Ga Sheikh Abduljabbar

Babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad. An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su. Daga cikin tuhumar da ake masa, hadda zargin wa’azinsa zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano. Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya dage zaman kotun don…

Cigaba Da Karantawa

Akwai Gyara A Harkar ‘Yan Kannywood – Adam Zango

Shahararren dan wasan Hausa fim na masana’atar Kannywood Adam Zango ya bayyana cewar da akwai gyara a yadda harkar ta su ke tafiya a halin yanzu da ya kamata a ɗauki matakin gyara. Adam Zango na bayani ne a yayin mayar da martani dangane da sukar da malaman addini da sauran jama’a ke yi musu na bata tarbiyya maimakon gyaranta. Jarumin ya ce tabbas idan har ɓera da sata babu shakka daddawa ma ta wari, yadda harkar ‘yan fim ke tafiya a yanzu abin takaici ne, an kai ga matsayin…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Masari Ya Sallami Shugaban Jami’ar Umaru Yar’adua

Labarin dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar Majalisar Zartaswa Jihar Wadda Gwamna Aminu Bello Masari ke Jagoranta ta Amince da Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina Farfesa Sanusi Mamman ya gaggauta Ajiye muƙaminsa, Sauke shi daga muƙamin ya biyo bayan Rahotan da Gwamna ya kafa ne ya ba shi shawara, kan Rahotan da aka gabatar mashi akan Korafe-korafe da aka gabatar akansa. Mai baiwa Gwamna Shawara kan Ilimi mai Zurfi, Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da maanema…

Cigaba Da Karantawa

KADUNA: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Nasarar Takarar Uba Sani

Kotun daukaka kara dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da karan da Sani Sha’aban ya shigar kan nasarar dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a zaben fidda gwanin gwamnan jam’iyyar da aka gudanar a jihar. Kotun ta ce ta fahimci cewa, daukaka karar an yi ta ne ba bisa ka’ida ba, kuma bata cika abin da ake bukata na cancanta bisa dalilin haka ta yi watsi da ƙarar tare da tabbatar da nasarar Sanata Uba Sani. Sha’aban ya daukaka kara ne…

Cigaba Da Karantawa

Jirgin Yakin Zaben Atiku Zai Dira Jíhar Anambra Yau Alhamis

Rahoton dake shigo mana daga jihar Anambra na bayyana cewar Jam’iyyar PDP tace shiri ya yi nisa na karban ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, a jihar ranar Alhamis domin gangamin yakin neman zaɓe. Daraktan kamfen Atiku/Okowa na jihar Anambra, Dakta Obiora Okonkwo ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai ranar Laraba a Awka. Yace wannan gangamin kaddamar da yakin neman zaben PDP da zai guda a Awka a yau zai tabbatar wa duniya cewa Anambra ta PDP ce gaba ɗaya babu maganar wata Jami’yya. Okonkwo yace jirgin…

Cigaba Da Karantawa

Na Yi Dukkanin Abin Da Zan Iya A Shugabancin Najeriya – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi iya bakin kokarinsa a matsayinsa na shugaban Najeriya. Shugaban ya shaida hakan ne a Amurka lokacin da yake tarban Sakatare Janar na kungiyar Abu Dhabi, Sheikh Al- Mahfoudh Bin Bayyah da mataimakinsa, Fasto Bob Roberts na Amurka, a wata ziyarar da suka kai masa. Buhari ya ce Najeriya kasa ce mai yawan al’umma da ke fuskantar kalubale daban-daban, sai dai a tsawon shekarun mulkinsa ya san cewa ya yi…

Cigaba Da Karantawa