Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar wata mata mai juna biyu, Mary Barka ta rasa ranta yayin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, dauke da bindigu kirar AK 47 suka yi dirar mikiya kauyen Pelachiroma na karamar hukumar Hawul dake jihar Borno. Ba tare da jinkiri ba shugaban mafarautan yankin Muhammad Shawulu Yohanna yayi nasarar cafkesu gami da mika su ga shugaban ‘yan sandan yankin Hawul, Habila Lemaka. Kamar yadda Yohanna, shugaban ‘yan sa kai da mafarauta ya bayyana…
Cigaba Da KarantawaDay: December 14, 2022
Rashin Albashi: Ma’aikata Sun Tsunduma Yajin Aiki A Jihar Filato
Labarin dake shigo mana daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Ma’aikatan gwamnati a jihar sun shiga yajin aikin jan kunne na kwanaki biyar wanda ya fara a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba Ma’aikata sun yanke shawarar daina aiki na wucin-gadi bayan gwamnatin ta ki biyansu albashi tsawon watanni uku. Ma’aikatan sun kuma yanke shawarar tafiya yajin aiki saboda gazawar gwamnatin wajen sakin kudaden da ake ragewa kamar su kudaden fansho, garatuti da sauransu. A wani taron manema labarai da ya gudana a Labour House da ke…
Cigaba Da Karantawa2023: Gwamna Inuwa Ya Roki Gwambawa Da Yin Sak
Labarin dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya roki jama’ar jihar su garzaya su karÉ“i Katin zabensu domin samun damar kaÉ—a wa APC kuri’unsu a 2023. Gwamnan yace É—umbin ayyukan da ya zuba a mulkinsa na farko babban alama ce dake nuna dacewarsa musamman yadda ya maida hankali wajen yaye matsin da mutane ke ciki. Inuwa Yahaya ya yi wannan jawabin ne yayin kamfe a gundumomi 5 da suka haÉ—a Ć™aramar hukumar Balanga ta arewa ranar Litinin. Da farko, gwamnan ya…
Cigaba Da KarantawaMatsalar Mai: Majalisa Ta Ba NNPC Wa’adin Mako Guda
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci kamfanin mai na kasa NNPC ya kawo karshen karancin fetur da ake fama da shi a cikin cikin mako guda. A cewar majalisa tsawon watanni ‘yan Najeriya na wahalar fetur wanda ke tasiri ga tattali arzikin kasa da jefa al’umma cikin wahala. Sannan kamfanin na bijiro da wasu dalilai a matsayin hujjar wahalhalun mai a fadin Najeriya, don haka wanna gargadi ne ga NNPC. Umarnin majalisa na zuwa ne bayan a karshen mako hukumar DSS ta bai…
Cigaba Da KarantawaZan Gina Sabuwar Najeriya Idan Na Zama Shugaban Kasa – Tinubu
Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar É—an takarar Kujerar zama shugaban kasa a inuwar jam’iyya mai mulki ta APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace da ikon Allah ‘yan Najeriya ba zasu yi da nasani ba idan suka zaÉ“e shi shugaban kasa a 2023. Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a wurin gangamin yakin neman zaÉ“ensa da ya gudana a Kaduna ranar jiya Talata. Gangamin Kaduna somin taÉ“i ne na fara yakin neman zaben shugaban kasa na APC a shiyya mafi yawan kuri’u a Najeriya watau…
Cigaba Da Karantawa