Ranar ‘Yanci: Kungiyar “Back To School” Yakar Cin Zarafin Mata Muka Sa A Gaba – Abdul Ahmad

Sakamakon ranar da majalisar ɗinkin Duniya ta ware na ranar ‘yanci ta duniya, wata Ƙungiya mai rajin kare yaƙin mata dake Kaduna wadda a turance ake kira da suna “Back To School” ta gudanar da taro a Kaduna domin jan hankali da wayar da kan jama’a akan cin zarafin Mata. Shugaban kungiyar Abdul Ahmad ya bayyana cewar dalilin shirya wannan taron nasu shi ne domin fadakarwar da wayar da kan jama’a musamman Mata domin sanin muhimmancin kansu da kuma kare kai daga dukkanin nau’ika na cin zarafi. Ahmad ya ƙara…

Cigaba Da Karantawa

Ba Zan Iya Zama Dan Majalisa Ba Saboda Ban Da Hakuri – El Rufa’i

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya nuna babu shi babu zuwa majalisar tarayya ta kasa bayan kammala wa’adin Mulki. An san Gwamnoni da yin takarar Sanata idan sun gama wa’adinsu a jihohi, sai dai anashi ɓangaren Malam Nasir El-Rufai yana cewa ya sha bam-bam da sauran gwamnoni yace bai da hakuri da jajircewar da ake bukata wajen aikin majalisa. Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron ‘yan majalisa da cibiyar nazarin aikin majalisa da damukaradiyya watau NILDS ta…

Cigaba Da Karantawa

Takaita Cire Kudi Zai Rage Wa ‘Yan Siyasa Sharholiya – Sanusi

Khalifa Muhammad Sanusi , ya ce matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na takaita cirar kudaden zai fi yin tasiri a kan `yan siyasa kasar fiye da talakawa. Ya bayyana hakan ne a karshen karatun Madaris da ya saba yi duk karshen mako. Ya ce `yan siyasar kasar na amfani da kudi a lokacin zabe don sayen kuri’un jama’a, lamarin da ke haifar da koma-baya ga kasar. Muhammadu Sanusi na II ya ce “abin takaici ne yadda mutane za su yi shekara hudu suna kwasar dukiyar al’umma, suna barin…

Cigaba Da Karantawa

Sai An Biya Miliyan 100 Kafin Mu Saki ‘Yan Matan Kwalejin Yawuri – ‘Yan Bindiga

Fitaccen ɗan ta’addan jihar Zamfara Dogo Gide da yayi garkuwa da dalibai mata ‘yan kwalejin Yawuri dake jihar Kebbi ya rantse ba zai saki sauran wadanda suka rage a hannunsa tare da malaman su har sai an kai masa diyyar naira miliyan 100 da ya bukata. Wannan matsayi ya biyo bayan wani sautin hirar da aka nada tsakanin wani daga cikin mahaifin dalibar dake hannunsa da mahaifiyarsa wadda ta bukaci ya sake sauran wadanda yayi garkuwar da su. Gide wanda yayi kaurin suna wajen kai munanan hare hare yana hallaka…

Cigaba Da Karantawa

Tinubu Ya Ziyarci Birnin Gwari Kafin Fara Kamfe A Kaduna

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ɗan takarar shugabancin ƙasa a karkashin jam’iyya mai mulki ta APC Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Birnin-Gwari kafin fara yakin neman zabensa a Kaduna. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da tawagarsa sun isa jihar Kaduna inda za su gudanar da yakin neman zabensa a jihar ta Kaduna a ranar Talata. Tinubun ya samu rakiyar abokin takararsa Sanata Kashim Shettima da babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon…

Cigaba Da Karantawa

Boko Haram: Karya Ce Babu Inda ‘Yan Ta’adda Za Su Boye A Sambisa – Atiku

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗan takarar shugabancin ƙasa a babbar jam’iyya adawa ta PDP Atiku Abubakar, yace duk ƙarya ce ake yi kawai, amma babu wani surƙuƙin dajin da ‘yan ta’adda za su iya ɓoyewa a Dajin Sambisa, a ce wai an kasa gano inda su ke. Atiku ya ce ya shiga dajin, amma babu komai daga ciyayi, sai kalage da gezoji kawai. Ya ce kan sa na ɗaurewa ganin yadda ake ta gaganiya da Boko Haram, amma an kasa ganin bayan su…

Cigaba Da Karantawa