Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Kotun Shari’ar Musulunci da ke birnin ta saka ranar 15 ga watan Disamban 2022 don yanke hukunci kan tuhume-tuhumen da ake yi wa malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara. Gwamnatin Kano na tuhumar shehin malamin da yin ɓatanci ga Annabin Musulunci Muhammadu S.A.W. kuma an tsare shi tun daga watan Yulin 2021. Abduljabbar zai sake bayyana a gaban Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola na kotun da ke Ƙofar Kudu ne bayan ƙungiyar lauyoyi masu bai wa marasa gata kariya ta…
Cigaba Da KarantawaDay: December 12, 2022
Na Bar PDP Har Abada – Obasanjo
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, a ranar Asabar, ya bayyana cewa ba zai taba komawa jam’iyyar adawa ta PDP da siyasa ba gaba daya a rayuwarsa. Ya bayyana hakan ne yayin hira da shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu da sauran masu fada a ji a jam’iyyar da suka ziyarcesa ranar Asabar bayan ganawar sirrin da suka yi, a gidansa dake birnin Abeakuta na jihar Ogun. “Na fita harkar siyasa kuma babu abinda zai iya mayar da ni. Duk wanda ke son shawarata, zan bada saboda amfanin Najeriya.” “Duk abinda nayi…
Cigaba Da KarantawaZan Yi Mulki Na Adalci Idan Na Lashe Zabe – Tinubu
Labarin dake shigo mana daga birnin Ibadan na Jihar Oyo na bayyana cewar a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya ba yan Najeriya tabbacin cewa zai zamo mai gaskiya da adalci ga kowa. Tinubu ya bayar da tabbacin ne yayin da yake jawabi a wani taro da shugabannin Musulunci daga kudu maso yamma a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ƙarshen mako. Dan takarar na APC ya yaba ma shugabannin addini a kasar kan addu’o’i da suke ci gaba…
Cigaba Da KarantawaShekau Ya Mutu Ya Bar Mata 83 A Duniya – Kwamandojin Boko Haram
Rahotannin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar wasu tsoffin Kwamandojin Boko Haram sun sanar da cewar shugabansu Abubakar Shekau ya mutu ya bar kwarkwara 83, lokacin da ya bar duniya. Mai ba Gwamnan Jihar Borno shawara a kan harkokin tsaro, Janar Abdullahi Ishaq ya sanar da wannan labari, yayin da ya bayyana cewar wasu tubabbun Kwamandojin Boko Haram da suka aje makamansu ne suka shaida masa. Janar Ishaq ya ce lokacin da suka karbi wasu daga cikin tubabbun a garin Bama ne daya daga…
Cigaba Da KarantawaBuhari Bai Da Masaniya Kan Kwamitin Da Gudaji Ke Ikirarin Shugabanta – Garba Shehu
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan wani ikirari da kwamiti na musamman da shugaban kasar ya kafa domin ya gudunar da bincike a kan cajin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki ƙarƙashin jagorancin Honorabul Gudaji Kazaure. Shugaban kwamitin, Gudaji Kazaure ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna kokarin hana ruwa gudu game da aikin nasa, da kuma hana shi ya mika wa shugaba Muhammadu Buhari rahotonsa. A cewar kwamitin wanda aka dora…
Cigaba Da Karantawa