Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce za ta mayar da rumfunan zabe 357, PUs, zuwa wuraren da babu tsaro saboda kalubalen tsaro a jihar Katsina. A cewar hukumar, ta dauki matakin ne domin bai waduk ‘yan gudun hijira, da ke jihar damar kaÉ—a kuri’unsu a zaben 2023. Kwamishinan zaÉ“e na jihar, Farfesa Ibrahim Yahaya Makarfi ne ya bayyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a yau Juma’a a Katsina. Ya bayyana cewa, dokar zabe ta 2022 ta yi tanadin tsare-tsare a bayyane da…
Cigaba Da KarantawaDay: December 11, 2022
Bauchi: An Damke Malamin Da Ya Soki Izala Kan Harka Da ‘Yan Siyasa
Labarin dake shigo mana daga jihar Bauchi na bayyana cewar Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar sun kama gami da tsare wani malamin addinin musulunci mazaunin garin Bauchi mai suna Abubakar Baba Karami bisa zarginsa da wasu kalamai kan ‘kungiyar izala inda ya nuna malamanta suna mu’amala da ‘yan siyasa. Malamin wanda aka fi sani da Afakhallah yayi wannan maganar ne akan mumbarin masallacin Juma’a a wani masallaci a jihar Bauchi a ranar 18 ga watan Nuwanban 2022. Ya bayyanna sunan Kabir Muhammad Gombe da Abdullahi Bala Lau da Ahmed Sulaiman…
Cigaba Da KarantawaDalilina Na Yin Kisa Da Garkuwa Da Mutane – Turji
Rahotannin dake shigo mana daga Gusau fadar Gwamnatin JÃhar Zamfara na bayyana Tashar Trust TV ta zanta da kasurgumin jagoran ‘yan bindiga Bello Turji, inda ya bayyana dalilin da yasa ya dau bindiga ya fara ta’addanci. A cewarsa, rashin adalcin da akewa Fulani Makiyaya da wulaÆ™anta su tare da mayar dasu Saniyar ware cikin al’umma ya tilasta masa daukar bindiga domin É—aukar fansa. A hirar, ya bayyana cewa a kasuwar Shinkafi ya fara ganin yadda aka yiwa dan Adam yankan rago. Yace jami’an Yan Sa Kai suka kawo wani mutumi…
Cigaba Da KarantawaZa A Rufe Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira – Gwamnatin Tarayya
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya Æ™arÆ™ashin jagorancin shugaban Æ™asa Muhammadu Buhari ta ce tana shirin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin Æ™asar. Babbar kwamishiniya a ma’akatar kula da ‘yan gudun hijira da kuma ‘yan cirani, Imaan Sulaiman-Ibrahim ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a yayin raba wa ‘yan gudun hijra guda 100 kayakin yin sana’o’i a wasu sansanoni da ke Abuja, babban birnin Æ™asar. Ta ce wadanda aka raba wa kayayyakin suna samun horo a fannin sana’o’i daban-daban domin samun kwarewa.…
Cigaba Da KarantawaBuhari Zai Tafi Amurka Halartar Taron Shugabannin Afirka A Yau
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasaMuhammadu Buhari a yau Lahadi zai tafi Amurka domin halartar taron shugabannin Æ™asashen Afirka da Amurka za ta karbi bakunci. A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kafofin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar yau Asabar, ya ce taron wanda za a gudanar daga ranar 13 zuwa 15 ga watan Disamba da shugaba Biden zai jagoranta, na da zimmar ganin ta yi aiki da gwamnatocin Afirka da kuma al’ummomin su da ke zama…
Cigaba Da Karantawa