Al’ummar unguwar Hotoro Danmarke a jihar Kano sun fada matsalar ruwa sakamakon rufe sayar da ruwa da ƴan garuwa su ka yi a yankin da kewayensa. Masu sayar da ruwan sun yanke shawarar ne bayan da wasu mazauna yankin su ka daki wani ɗan garuwa sabo da ya ƙi sayar musu da ruwa. Wani mai sayar da ruwa, Malam Yahuza Lawan, wanda ya shaida lamarin ya ce sun yanke shawarar daukar matakin ne saboda wasu mazauna yankin sun lakaɗa wa ɗan uwansu dukan tsiya. A cewar Lawan, wani mazaunin unguwar…
Cigaba Da KarantawaDay: December 10, 2022
Nasarawa: Matasa Sun Yi Wa Shugaban APC Ature
Rahotannin dake shigo mana daga Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewar wasu fusatattun Matasa sun yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ihu a yayin wani gangamin taron Jam’iyyar da ya gudana a jihar. Shugaban IPAC mai kula da harkar jam’iyyu a jihar Nasarawa, Cletus Ogah Doma ya yi tir da abin da Matasan suka aikata inda yace ko kaɗan wannan ba abu ne da za a lamunce sake faruwar hakan anan gaba. Sai dai ya yi ƙarin haske akan labarin da ake yaɗawa na…
Cigaba Da KarantawaFina-Finai: Marigayi Ibiro Ya Cika Shekaru Takwas Da Rasuwa
An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar 1971. Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan da ke cikin karamar hukumar Warawa. Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon malamai ta Wudil (Teachers College). Daga nan ne ya shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a shekarar 1991. Ya yi shekara takwas Ya na aikin Gandiroba inda ya kai matakin insfekto, daga nan ne ya bari ya cigaba da sana’ar wasan kwaikwayo. Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar Fim a tun ya na aji uku na makarantar sakandare. Ya na…
Cigaba Da KarantawaMun Tura Sabbin Takardun Naira Bankuna – Gwamnan Babban Banki
Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, CBN, Godwin Emefiele, ya ce sabbin takardun kudi na Naira da aka canja wa fasali tuni sun isa bankuna kuma su na jiran a bada umarnin fara fitar da su. A cewar wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafinsa na Twitter, Emefiele ya bayyana haka ne a Daura yayin da ya kai ziyarar yi wa shugaban kasa Muhanmadu Buhari karin bayani kan sake fasalin kudin Naira da kuma manufar hada-hadar kuɗi ta hanyar sadarwa da aka sake dawo da ita. Ya ce sake fasalin kudin…
Cigaba Da KarantawaSojoji Na Shan Matsin Hada Baki Da ‘Yan Siyasa A Yi Murdiya – Babban Hafsan Tsaro
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ya yi iƙirarcewa ba tun yau ba, an daɗe ana yi wa sojoji da sauran jami’an tsaro romon kunne su haɗa baki a murɗe zaɓe. Sai dai kuma Irabor ya ce sojoji tsaye su ke ƙyam a wuri ɗaya, a tsakiya, ba su goyon bayan kowace jam’îyya, kuma babu ruwan su da kowane ɗan takara. “Tabbas a kowane zaɓe tun bayan dawowar mulkin dimokraɗiyya a 1999, sojoji na fama da matsin-lamba daga…
Cigaba Da Karantawa