Ku Taya Mu Tsare Ofisoshinmu: Rokon INEC Ga ‘Yan Najeriya

Shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta Farfesa Mahmood Yakubu ya roƙi al’ummar Najeriya su taimaka wurin kare kadadrorin hukumar gabanin babban zaɓen ƙasar mai zuwa. Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai wa wasu ofisoshin hukumar a baya-bayan nan. Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da ƙungiyar dattijan yammacin Afirka, a ofishinsa da ke Abuja, a ranar Litinin. Shugaban na INEC ya ce babban abin da ake fargaba gabanin zaɓen mai zuwa shi ne matsalar tsaro. Ya ce “an kai hari a ofisoshinmu…

Cigaba Da Karantawa

An Samar Da Maganin Ciwon Zazzabin Lassa A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar da ke inganta tsirrai da dabbobi ta Najeriya ta ce ta yi nasarar samar da maganin zazzabi Lassa, wanda ke halaka al`umma a wasu kasashen Afirka, ciki har da Najeriya. Zazzabin Lassa dai ba shi da wani magani sadidan, cuta ce wacce ta daɗe tana kisa a Najeriya wadda aka tabbatar da ɓeraye ne ke haddasa ta. Amma yanzu hukumar ta ce jami`anta sun gano maganin, bayan shafe shekara shida suna gudanar da bincike, kuma a halin da…

Cigaba Da Karantawa

Jajirtaccen Shugaba: Kasar Guinea Bissau Za Ta Karrama Buhari

Gwamnatin Guinea Bissau za ta karrama shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da lambar girmama mafi a kasar. Za ta karrama shugaba Buharin ne bisa la’akari da gudummuwar da yake bayarwa wajen daidaitawa da bunkasa demokuradiyya a shiyyar Afirka ta yamma. Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoko Embalo shi ne zai lika wa shugaba Buharin lambar yabon, a wani gagarumin biki da aka shirya a kasar. Wata sanarwar da mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan harkar yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce gwamnatin Guinea Bissau din ta yanke…

Cigaba Da Karantawa

Babban Bankin Kasa Ya Takaita Adadin Kudin Da ‘Yan Najeriya Za Su Cire A Bankuna

Babban bankin Najeriya CBN ya fitar da sababbin dokoki na hada-hadar kuɗaɗe a bankunan ƙasar. A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, CBN ya taƙaita yawan kuɗade laƙadan da ƴan ƙasar za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki. Wannan sanarwa na zuwa ne mako biyu bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun naira da aka sabunta. Sabbin matakan da CBN ɗin ya fitar a ranar Talata sun haɗa da: Yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Za Ta Cimma Burin Fitar Da Adadin Man Fetur A Kasuwannin Duniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ƙaramin ministan man fetur Timipre Sylva ya sanar da cewa zuwa mayun shekara mai zuwa, Najeriya za ta cimma burin Kungiyar Kasashen Duniya masu azrikin man fetur OPEC domin fitar da gangar mai miliyan daya da dubu dari takwas. Wata sanarwa da mai ba ministan shawara kan harkokin yaɗa labarai Horatius Egua ya fitar, ministan ya ce Najeriya za ta yi iya kokarinta domin ƙara tsaurara tsaro kan manyan hanyoyin da bututun mai na ƙasar suke da kuma toshe…

Cigaba Da Karantawa