Kotu Ta Saki Dalibin Da Ya Wulakanta Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta janye ƙarar da shigar kan wani dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, Aminu Mohammed, wanda ya kammala karatu a shekarar karshe bayan matsin lamba da kuma da alla-wadai da ga sassan kasar. Da ya ke janye karar a yau Juma’a, lauyan masu shigar da kara, Fidelis Ogbobe, ya ce uwargidan shugaban kasa a matsayinta na uwa a kasa ta yanke shawarar janye karar, biyo bayan maganganu da ƴan Najeriya masu kishi su ka yi. Ya dogara da Sashe na 108 karamin sashe na 2 (a)…

Cigaba Da Karantawa

INEC Ta Sanya Ranar Fara Raba Katinan Zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, a ranar Juma’a ta sanar da cewa ‘yan kasa da suka yi rijistar katin zabe kafin zuwan zaben 2023 zasu fara karba katin zabensu na dindindin daga ranar 12 ga watan Disamban 2022. Wannan na kunshe ne a takardar da aka bai wa manema labarai a Abuja. Kamar yadda takardar tace, hukumar tayi taro a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamban 2022 kuma suka tattauna kan wasu muhimman abubuwa da suka hada da fara karbar katinan zabe a fadin kasar nan. An…

Cigaba Da Karantawa

Al-Mundahana: Buhari Ya Kori Shugaban Hukumar NIRSAL

An tsige Manajan Darakta na Hukumar rarraba tallafi a fannin Aikin Gona na kasa (NIRSAL) daga aikinsa. Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito Majiyar Dimokuradiyya ta nakalto cewa korar Aliyu Abdulhameed, ba zai rasa nasaba da zarge-zargen cin hanci da rashawa da yawa ba. A watan Janairun bana ne Daily Trust ta gudanar da bincike kan yadda NIRSAL ke bayar da lamunin rancen biliyoyin Naira na wasu kamfanoni masu zuba jari don noma hekta 20,000 na alkama na noman rani a Kano da kuma Jigawa bisa zargin karkatar da…

Cigaba Da Karantawa

Shugaban ‘Yan Sanda Ya Nemi Kotu Ta Janye Hukuncin Daurin Da Ta Yi Mishi

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya shigar da ƙudirin neman jingine umarnin kotu da ya ɗaure shi wata uku a gidan yari, yana mai cewa bai raina umarnin kotun ba. Cikin ƙorafin da ya gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja ranar Alhamis, shugaban ‘yan sandan ya ce ba a ƙarƙashin shugabancinsa aka aikata laifin da kotun ta yi hukunci a kansa ba kuma “ba a saɓa wa umarnin kotu ba”. A makon nan ne Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin kama babban…

Cigaba Da Karantawa

Aisha Buhari Ta Janye Karar Da Ta Kai Amìnu Muhammad

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta janye karar da ta shigar da Aminu Muhammad a kotu. Uwargidan shugaban na neman kotu ta bi mata kadinta ne kan kalaman bata suna da take zargin Muhammad ya wallafa a kanta a shafinsa na sada zumunta. A watannin baya, Muhammad ya wallafa wani sakon Twitter da ke cewa, “mama an ci kudin talakawa an koshi,” hade da hotonta. Hakan ya sa a ranar 18 ga watan Nuwamba, jami’an tsaro suka kama Muhammad,…

Cigaba Da Karantawa