Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya da ke zama a Minna, jihar Neja, ta bayar da umurnin kama babban hafsan sojin kasa Janar Faruk Yahaya bisa laifin rashin grimama kotu. Mai shari’a Halima Abdulmalik, wadda ta yanke hukuncin ta kuma bukaci da a kulle Janar Yahaya a gidan gyara hali na Minna saboda saba ma wani umurnin kotu na ranar 12 ga watan Oktoba, 2022. Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wata babbar kotun da ke zamn ta a…
Cigaba Da KarantawaDay: December 1, 2022
Kano: An Janye Dokar Hana ‘Yan A Daidaita Sahu Hawa Manyan Tituna
Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta janye dokar da ta hana ƴan adaidaita-sahu bin wasu manyan tituna cikin kwaryar Kano. Shugaban Hukumar kula Da Zirga-zirgar Ababen-hawa, KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Kano. Ya ce an janye dokar ne saboda matuƙa baburan adaidaita-sahu ɗin sun yi biyayya kuma al’umma sun yi suka a kan dokar.
Cigaba Da KarantawaAn Amince Da Koyar Da Yara Karatu Da Harsunan Gida A Makarantu
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar ministoci ta amince da wata manufa kan amfani da harsunan gida wajen koyar da dukkan daliban kasar a matakin firamare a fadin kasar. Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da haka ga manema labarai, bayan taron majalisar ministoci da aka yi a ranar Laraba cewa majalisar ta amince a aiwatar da sabon tsarin amfani da harsunan gida da ake kira National Language Policy wanda ma’aikatarsa ta kirkiro. Ministan ya bayyana cewa ” ka’idojin koyarwa na shekaru shida na farko a…
Cigaba Da KarantawaTsohon Dan Wasan Kwallon Brazil Pele Na Kwance Rai A Hannun Allah
An kwantar da shahararren dan kwallon Brazil Pele a asibiti amma ƴarsa ta ce baya cikin mummunan yanayi. Tashar ESPN Brasil ta bada rahoton cewa an garzaya da Pele zuwa asibitin Albert Einstein da ke birnin Sao Paulo saboda yana fama da kumburi a jikinsa. Amma diyar Pele din Kely Nascimento ta wallafa a shafinta na Instagram cewar jikin bai yi tsanani ba. A watan Satumbar 2021 ne aka yi wa Pele tiyata kuma tun daga lokacin ake yawan kwantar da shi a asibiti. ESPN Brasil ta bada rahoton cewa…
Cigaba Da KarantawaKotu Ta Daure Dalibin Da Ya Ci Zarafin Aisha Buhari
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da cin mutuncin Uwargidan Shugaban ƙasa Aisha Buhari gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari. Lauyan dalibin CK Agu ya tabbatar wa da BBC cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba. Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a bada Aminu beli…
Cigaba Da KarantawaGwamnoni Ne Suka Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Talauci – Fadar Shugaban Kasa
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta dora alhakin katutun talaucin da ke damun Najeriya kan gwamnonin jihohi. Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Clem Agba ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya ranar Laraba, kamar yadda gidan talbijin na Channels TV ya rawaito. Ya ce shirin gwamnatin tarayya na kyautata rayuwar ‘yan kasar bai yi tasirin da ya kamata ba ne saboda gwamnonin jihohi ba su bai wa gwamnatin tarayya hadin kai ba.…
Cigaba Da Karantawa