Kotu Ta Yanke Wa Sifeto Janar Na ‘Yan Sanda Daurin Watanni Uku A Kurkuku

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Talata ta yanke wa Sufeto-Janar, IGP, na ƴan sanda, Usman Baba, zaman gidan yari na tsawon watanni uku, bisa zargin kin bin umarnin hukuncin da wata kotu ta yanke na kin mayar da wani jami’in dan sanda, Patrick Okoli, wanda aka yi wa ritaya ta ƙarfi da yaji bakin aiki. Mai shari’a Bolaji Olajuwon, a hukuncin da ya yanke kan karar da lauyan Okoli, Arinze Egbo, ya shigar, ya kuma gargadi Baba kan rashin bin hukuncin da kotun farko ta yanke…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Sanda Sun Nesanta Kansu Da Kama Matashin Da Ya Soki Aisha Buhari

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa, tace ba ta da hannu wajen cafke wani dalibi mai suna Aminu Muhammad da ake zargin tayi. Ana zargin Aminu Muhammad yana hannun dakarun ‘yan sanda bisa zargin da ake yi masa na cin mutuncin uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari. Da aka tuntubi ‘yan sandan jihar Jigawa, sun tabbatar da cewa Aminu Muhammad bai hannunsu, kuma ba su iya yin wani bayanin inda ya shiga ba. Kakakin rundunar jihar, DSP Lawan Shiisu ya shaidawa manema labarai cewa bai da labarin jami’an sanda sun dauke…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Mata 721 Aka Yi Wa Fyade Cikin Watanni Tara – Hukumar Kare Hakkin Dan Adam

Hukumar kare hakkin dan adam a jihar Kano ta ce cikin watanni tara sun karbi bayanan aikata fyade har 721 daga sassan jihar. Shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa cibiyar da ke lura da wadanda aka yi wa fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata mai suna WARAKA ce ta tantance tare da bin diddigin al’amarin. Fyaɗe, matsala ce da ke ƙara ƙamari a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar fyaden. Cibiyar WARAKA ta karbi korafin aikata fyade da sauran nau’ukan cin zarafin…

Cigaba Da Karantawa

Likitoci Sun Bukaci Sanya Hannu A Dokar Kare Hakkin Mata

Ƙungiyar likitoci masu lura da lafiyar mata ta ƙasa ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya sanya hannu kan dokar kare lafiyar mata da jarirai. A cewar ƙungiyar hakan zai zamo wani abin tarihi, wanda al’ummar ƙasar ba za su manta da shi ba. Shugaban ƙungiyar, Dr Habib Sadauki ne ya buƙaci hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi. Sadauki ya ce dokar za ta taimaka wajen rage mutuwar mata masu juna-biyu da jarirai. Ya ƙara da cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da…

Cigaba Da Karantawa

Cushe A Kasafin Kudi: An Raba Rana Tsakanin Ministar Jin Kai Da Ministar Kudi

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar batun yi wa kasafin kudin 2023 ciko da majalisar dattawan ke tuhumar ma’aikatar kudi na ci gaba tayar da kura. Kan wannan batun, Ministar jin kai ta aika wa takwararta ta ma’aikatar kudi wata wasika wadda a ciki ta dora alhakin bayyanar wasu naira biliyan 206 cikin kasafin kudin ma’aikatarta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin wadannan ma’aikatun gwamnatin biyu. A makon jiya, yayin da ministar jin kai ta halarci zaman majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma’aikatarta,…

Cigaba Da Karantawa

APC Ta Tafka Babbar Asara: Surukin Buhari Ya Fice Daga Ciki

Jam’iyyar APC ta rasa daya daga cikin yan takararta na gwamna a jihar Kaduna, Sani Sha’aban Sha’aban wanda suruki ne ga shugaban kasa Buhari ya rasa tikitin takara a hannun Sanata Uba Sani. A ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba, Sha’aban ya sanar da ficewarsa daga APC a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu, kuma aka rarraba ta ga manema labarai. Ya ce harkokin jam’iyyar ne suka sanya shi yin murabus, yana mai zargin cewa maimakon shayar da mutane romon damokradiyya, wasu yan tsiraru a APC reshen Kaduna sun…

Cigaba Da Karantawa