Katsina: An Damke Matar Da Ta Jefa Dan Kishiyarta A Rijiya

Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta kama Maryam Habibu, ƴar shekara 18 da haihuwa, bisa zarginta da jefa ɗan kishiyarta mai shekaru hudu cikin rijiya a ƙaramar hukumar ƙafur ta jihar. Maryam wadda ta fito daga ƙauyen Leko da ke ƙaramar hukumar Ɗanja tare da wasu mutane 11 da ake tuhuma da laifuka daban-daban da suka haɗa da fashi da makami da satar shanu, an gabatar dasu a ranar Juma’a a shelkwatar ƴan sanda da ke Katsina. Kakakin rundunar ƴan sandan, SP Gambo Isah, yayin da yake zantawa da…

Cigaba Da Karantawa

Taraba: Kotu Ta Tabbatar Da Kefas Agbu A Takarar Gwamna Na PDP

Kotun daukaka kara dake da zamanta Yola, a Jihar Adamawa ta tabbatar da Laftanar Kanar Kefas Agbu (ritaya) a matsayin dantakaran Gwamnan PDP a Taraba. Hukuncin na zuwane biyo bayan karan da Farfesa Jerome Nyameh ya shigar yana mai kalubalantan hukuncin Babban Kotun Gwamnatin Tarayya dake da zamanta a Jalingo yanke na tabbatar da Kefas a matsayin sahihin dan takaran Gwamnan Jihat Taraba a Jam’iyyar PDP Kotun daukaka kara dake Yola, ta kara fatali da karan da Hilkiah Bubajoda Mafindi, daya daga cikin wanda aka fafata zaben fidda gwanin PDP…

Cigaba Da Karantawa

Rabin Albashi: ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar malaman jami’a (ASUU) ta yi wata kwarya-kwaryar zanga-zanga kan rikicinta da gwamnatin tarayya da kuma rashin biyansu cikakken albashi a watan da ya gabata. ASUU ta ce wannan zanga-zanga sun yi ta ne don nuna damuwa ga yadda ake yiwa Malaman rikon sakainar kashi da kuma alanta tsarin ‘ba aiki ba albashi a kansu’, da kuma tursasa su su koma bakin aiki ba tare da samun hakkinsu ba. Kungiyar ta ce, matukar gwamnati ta gaza biya musu bukata,…

Cigaba Da Karantawa

2023: INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka’idoji Ga Jam’iyyu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gabanin babban zaben shekarar 2023, Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta gargadi yan takara da yan siyasa su daina kamfen a wuraren ibada da hukumomin gwamnati. Kazalika, an kayyade Naira miliyan 50 a matsayin kudi mafi yawa da daidaikun mutane ko kungiya za su iya bawa dan takara. Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da INEC ta fitar a Abuja ta hannun kwamishinanta kuma direkta na kwamitin labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye. Bisa wannan…

Cigaba Da Karantawa

Mun Yi Nasara A Shari’o’i Fiye Da 3000 A Bana – EFCC

Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a ta ce ta yi nasara a shari’o’i 3,328 da ta gurfanar da mutanen da take zargi da cin hanci cikin wata 11 na shekarar 2022. Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa ya zuwa 18 ga watan Nuwamba 2022, sun yi nasarar ƙwace kuɗi naira miliyan 755 daga hannun tsohon babban akanta na ƙasa waɗanda suka mayar wa gwamnati. Kazalika, EFCC ta ƙwace kadarorin alfarma uku daga hannun Kanar Bello Fadile (mai ritaya) – tsohon mataimaki na musamman ga tsohon…

Cigaba Da Karantawa

Siyasa Ba Da Gaba Ba: Tinubu Ya Taya Atiku Murnar Ranar Haihuwa

Ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu, ya taya abokin hamayyarsa na PDP Atiku Abubakar murnar cika shekara 76 da haihuwa. A ranar Juma’a ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar kuma haifaffen Jihar Adamawa da ke arewacin ƙasar ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar tasa. “Ina taya Atiku Abubakar murnar ranar haihuwarsa ta 76,” in ji Tinubu cikin wani saƙon Twitter. “Ina yi masa fatan alheri.” Wannan ne karo na shida da Atiku zai yi takarar shugaban ƙasa bayan ya yi rashin nasara a 1993, da 2007, 2011, da…

Cigaba Da Karantawa