Arewa Maso Yamma Na Fama Da Gagarumar Matsalar Rashin Lafiya – Likitocin Duniya

Kungiyar likitocin duniya ta Medecins Sans Frontieres (MSF) ta ce arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar gagarumar matsalar kiwon lafiya. Kungiyar ta ce kananan yara masu dimbin yawa suna fuskantar matsalar tamoiwa. MSF ta bayar da kulawa ga kananan yara 100,000 da ke fama da tamowa tun daga farkon shekarar nan, tana mai cewa kimanin yara 17,000 suna bukatar kulawar asibiti. Kungiyar ta kara da cewa taimakon da ake bai wa yaran ya yi matukar kadan, domin kuwa an mayar da hankali kan yankin arewa maso gabashin kasar inda ake…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Mikel Obi Ya Yi Ritaya Daga Kwallon Kafa

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa na Najeriya Mikel John Obi ya sanar da ritayarsa daga wasan kwallon kafa. Mikel Obi ya sanar da matakin ne ranar Talata a shafinsa na Instagram. Ya lashe gasar Zakarun Turai a 2012 tare da tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea, baya ga wasu jerin kofunan da ya lashe, kuma a baya-bayan nan yana buga wa kungiyar Kuwait SC ne. Ga wani abu cikin sakon da ya wallafa a Instagram: “Akwai wani karin magana da ke cewa komai na da karshe kuma haka lamarin yake ga…

Cigaba Da Karantawa

Saudiyya: Sarki Salman Ya Nada Yarima Mai Jiran Gado Mukamin Firaminista

Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya ya nada dansa kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ga mukamin firaministan kasar sannan ya nada dansa na biyu Yarima Khalid a matsayin ministan tsaro, kamar yadda wata dokar da Sarkin ya sanya wa hannu ta sanar. Sauyin ya kuma bar Yarima Abdulaziz bin Salman a matsayinsa na ministan makamashi. Ministan harkoki da kasashen waje Yarima Faisal bin Farhan al Saud da ministan kudi Mohammed al-Jadaan da kuma ministan zuba jari Khalid al-Falih sun ci gaba da rike mukamansu. Yarima Mohammed bin…

Cigaba Da Karantawa

Babu Jihar Da Aka Amince Ta Sayo Makamai Masu Sarrafa Kansu – Fadar Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar Shugaban ƙasa ta fitar da wata sanarwa da ke cewa babu wata jihar da aka ba izinin sayo makaman yaki masu sarrafa kansu domin raba wa kungiyoyinsu na samar da tsaro. Sanarwar Fadar ta kuma ce ta dade tana nanata cewa babu mutumin da aka ba izinin mallakar bindiga iri samfurin AK-47 ko ma wata bindiga mai sarrafa kanta, inda ta ce tilas ne su mika irin bindigogin ga hukumomin tsaron kasar. Fadar ta kuma ce an ba…

Cigaba Da Karantawa