Talauci Ne Silar Jefa ‘Yan Najeriya Halin Da Suke Ciki – Abdulsalami Abubakar

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon shugaban ƙasa Janar Abdulsalami Abubakar ya ja hankalin ‘yan kasar kan muhimmancin kare ‘yancinsu da kuri’arsu a babban zaben 2023. Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake shirin gudanar da taron sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan takara na jam’iyyun siyasa gabannin yakin neman zabe. Taron zai kuma kunshi sauran masu ruwa da tsaki inda za a sanya hannu a rukuni biyu. Na gabanin fara yakin neman zabe da kuma gab da…

Cigaba Da Karantawa

Cunkoson Hanyar Kaduna Zuwa Abuja: Gwamnatin El Rufa’i Ta Koka

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasiru El Rufa’i ta nuna damuwa kan cunkoson da matafiya ke fuskanta a hanyar Kaduna zuwa Abuja babban birnin tarayyar kasar. Sanarwar da ta fitar ta ce yanzu haka suna kan tattaunawa da kamfanin Julius Berger da sauran masu ruwa da tsaki da ke aikin hanyar, don ganin an warware matsalar. Matafiya da ke bin ta Kaduna don zuwa Abuja da sauran biranen Najeriya na cin kwakwa, kafin su iya wuce matsanancin cunkoson da ke…

Cigaba Da Karantawa

Sama Jannati: Saudiyya Za Ta Tura Mace Ta Farko Sararin Samaniya

Hukumar kula da sararin samaniya ta Saudiyya ta ƙaddamar da shirin sama jannati a karon farko da ya haɗa da aika mace ta farko ƴar ƙasar zuwa sararin samaniya a 2023. Shirin zai mayar da hankali ne wajen horar da ƙwararru ƴan asalin Saudiyya don su yi tafiya mai nisan zango da mai gajeren zango a jirgin sama jannati zuwa sarrain samaniyar. Shirin zai bai wa ƴan sama jannati Saudiyya damar aiwatar da binciken kimiyya don ci gaban ɗan adam a ɓangarorin da suka fi muhimmanci kamar lafiya da ci…

Cigaba Da Karantawa

Ina Nan Daram A Jam’iyyar PDP – Wike

Rahoton dake shigo mana daga Fatakwal babban birnin Jihar Ribas na bayyana cewar Gwamnan jihar Nyesom Wike ya ce yana nan daram a PDP babu inda za shi, kuma zai cigaba da yaki don ganin an yi abin da ya dace. Ya fadi hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar da wakilan mazabu 319 na jihar Rivers, a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal. Ya ce babu gudu ba ja da baya, ba kamar yadda ake ta hasashe ba cewa zai iya barin jam’iyyar. ”Abin…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa Domin Fita Daga Tarnakin Bashi – Bankin Afrika

Shugaban bankin raya kasashen Afrika Akinwumi Adesina ya bayyana cewa Najeriya na bukatar taimako don warware basukan da suka dabaibayeta la’akari da yadda matsalar ke barazana ga ci gaban kasar ta yammacin Afrika. A jawabinsa yayin taron tattalin arziki da zuba jari a birnin New York Akinwumi Adesina wanda asalinsa dan Najeriya ne da ke jagorancin bankin, ya ce tarin bashi ya yiwa kasar katutu wanda ya zama babban kalubale gareta wajen gudanar da ayyukan ci gaba. A cewar Adesina ba kadai Najeriya, kasashen Afrika da daman a fama da…

Cigaba Da Karantawa