ASUU: Zan Sa Kafar Wando Guda Da Dalibin Da Ya Fito Zanga-Zanga – El Rufa’i

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar a ranar Talata, ta ce ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko wata kungiya na toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga ba. Kwamishinan tsaro na cikin gida a jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, inda ya ce ba za a amince da wannan matakin ba, kuma wani share fage ne na karya doka da oda. “Da wannan sanarwar, ana shawartar mutane ko ƙungiyoyin…

Cigaba Da Karantawa

2023: Ka Da Kuyi Gangancin Zabar Musulmai A Shugabancin Kasa – Dogara Ga Kiristoci

Tsohon shugaban majalisar Tarayya Yakubu Dogara ya gargaɗi Kiristocin Najeriya kada su barnata kuri’un su wajen zaɓen jam’iyyar APC, da ta tsaida musulmi ɗan takara, musulmi mataimaki. Idan ba a manta ba tun bayan sanar da Kashim Shettima ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC da Tinubu yayi Yakubu Dogara, Lawal Babachir da Sanata Elisha Abbo wanda duk ƴan Arewa ne suka fito karara suka soki abin. Bayan haka sun yi kira ga duka kiristocin Najeriya kada su zaɓi jam’iyyar APC domin ta tsayar da duka ƴan takaran ta…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aikin ASUU: Dalibai Sun Gudanar Da Zanga-Zanga

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗaliban jami’o’in Najeriya na ci gaba da zanga-zangar lumana a sassan ƙasar daban-daban biyo bayan yadda yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsawon lokaci. Ko a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ɗaliban sun toshe hanyar shiga filin jirgin sama na Murtala Muhammad tare da wasu manyan hanyoyi, wani lamari da ya haifar da cikas ga sufurin jiragen. Hakan dai wani ƙoƙari ne da suke yi domin matsawa gwamnatin ƙasar lamba don ta magance…

Cigaba Da Karantawa

2023: Hukumar Zabe Ta Fitar Jerin Sunayen ‘Yan Takara

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da majalisar dattawa da kuma na majalisar wakilai na dukkan jam’iyyun ƙasar da za su fafata a zaɓukan 2023. INEC ta fitar da jerin sunayen ne a ranar Talata, 20 ga watan Satumban 2022, inda ta ce jerin na ƙu she ne da sunayen ƴan takara daga jam’iyyu 18. An wallafa jerin sunayen na ƴan takara daga dukkan mazaɓun ƙasar a shafin intanet na INEC. Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da…

Cigaba Da Karantawa