2023: APC Na Shirin Tafka Magudi A Kano – NNPP

Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta zargi jam’iyyar APC da shirya yadda zata rage yawan masu kada kuri’u a jihar ta hanyar yaudara tare da kwace katinan zaben jama’a. Wannan ya faru ne a karo na farko a tarihin shugabancin jihar inda aka mayar da shugabanci zuwa gado kamar yadda NNPP tace sun bayyana a dokokin gwamnatin da nade-nadenta. “Ɗan takarar da gwamna ya zaba” ya rantse da Qur’ani kan cewa zai cigaba da barnar da ake a jihar Kano ba tare da dakatar da ita ba. Jam’iyyar ta yi…

Cigaba Da Karantawa

Jigawa: Ambaliyar Ruwa Ya Ci Rayuka 92

Rahoton dake shigo mana daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewar yawan wadanda ambaliyar ruwa yayi ajalinsu a jihar ya haura sama inda ya kai har mutum 92. Wannan yana zuwa ne yayin da Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, yake shan caccaka sakamakon shillawa kasar waje da yayi hutu ba tare da ziyartar wadanda ibtila’in ya fadawa ba. Kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Lawan Adam, ya tabbatar da cewa mutum 92 suka rasa rayukansu tsakanin watan Augusta zuwa Satumba sakamakon ambaliyar ruwa. Lawal Adam…

Cigaba Da Karantawa

Sakin Baki: Kotu Ta Ci Abduljabbar Tarar Miliyan 10

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Litinin, ta ci tarar malamin addinin Musulunci da ake tsare, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Naira Miliyan 10 bisa shigar da kara kan tabbatar da hakkinsa na ɗan ƙasa, inda kotun ta ce hakan rashin ɗa’a ne ga kotun. Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke, ya bayar da umarnin a biya wadanda ake kara kudaden; da su ka haɗa da Kotun Shari’a ta Kofa Kudu, Kano, da gwamnatin jihar Kano a matsayin waɗanda a ke kara na daya…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Yi Mummunan Ta’adi A Kudancin Kaduna

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar kungiyar mutanen kudancin Jihar wato SOKAPU ta yi zargin cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da sama da mutum 40, harda ‘yan coci a kwatas din Bayan Kasuwa da ke Kasuwan Magani, karamar hukumar Kajuru dake jihar ta Kaduna. A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr. Awemi Maisamari,ya gabatarwa manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, ya ce yan bindigar sun tuntubi yan uwan wadanda aka sace inda suke nemi a biya naira miliyan 200 kafin su sake su.…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnoni Ne Matsalar Dimokuradiyya A Najeriya – Ghali Na’abba

Tsohon shugaban Majalisar wakilan tarayya Ghali Umar Na’Abba ya zargi gwamnonin jihohi da zama barazana ga mulkin dimokiradya saboda matakan da suke dauka wadanda suka saba ka’ida. Na’Abba ya zargi gwamnonin da karbe iko da jam’iyyu wajen zama wuka da nama ta hanyar yin gaban kansu wajen bayyana wanda zai tsaya takarar zabe ko kuma wanda zasu nada domin rike mukamai daban daban. Tsohon shugaban majalisar yace tun daga shekarar 1999 gwamnonin suka zama kadangarun bakin tulu, wadanda suke taimakawa wajen murkushe dimokiradiya a cikin gida, abinda ke hana gabatar…

Cigaba Da Karantawa