Dalilin Da Ya Sa Na Kashe Ummu Kulthum – Dan Kasar Chaina

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Mutumin da ake zargi da kashe wata budurwa a Kano ɗan ƙasar Chaina Geng ya yi zargin cewa Ummu ta masa alƙawarin zata aure shi amma daga baya ta saɓa alƙawarin bayan ya kashe maƙudan kuɗi a kanta. A jawabin da ya yi wa yan sanda, Ɗan China ya bayyana cewa saɓa alƙawarin ya fusata shi sosai, bisa haka zuciyarsa ta raya masa ya je har gida ya kasheta. Mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano Kiyawa ya…

Cigaba Da Karantawa

Zunubi Ne Rama Marin Da Dan Sanda Ya Yi – Baturen ‘Yan Sanda

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa, ya bayyana cewa mutum bai da ikon ramawa koda ace dan sanda ya mareshi idan dai har ɗan sandan yana sanye da Inifam. Olumuyiwa Adejobi, ya ce abin da ya kamata mutum yayi shine ya kai kara gaban hukuma domin doka ta tsawatar masa. Mai magana da yawun yan sandan ya ce cin mutuncin jami’in dan sanda da ke sanye da kayan aiki tamkar cin mutuncin Najeriya. Kakakin ‘yan Sandan ya bayyana hakan…

Cigaba Da Karantawa

2023: Atiku Ya Nada Tsoffin Janarorin Soji Kwamandojin Yakin Neman Zabe

A wani shiri mai kama da yaƙin a-yi-ta-ta-ƙare, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, ya naɗa tsoffin Janar-Janar uku na soja a cikin Rundunar Kamfen ɗin Cin Zaɓen Shugaban Ƙasa . Aikin wannan Majalisar Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa shi ne ta shirya yadda za a yi yaƙin neman zaɓen 2023 na PDP. Ana kallon babban zaɓen shekarar 2023 dake tafe a matsayin wani zaɓe da zai yi tasiri a Najeriya tun bayan sake ayyana Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a PDP da tikitin musulmi da musulmi…

Cigaba Da Karantawa

Fitar Buhari Da Osinbajo: ‘Yan Najeriya Sun Shiga Rudanin Rashin Sanin Jagora

‘Yan Najeriya sun shiga cikin ruɗani na rashin sanin ko wanene ragamar ƙasa take a hannunsa yanzu biyo bayan ficewar Buhari da mataimakin sa Osinbajo daga kasar. Idan jama’a za su tuna Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cilla birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron majalisar ɗinkin Duniya karo na 77, yayin da Osinbajo ya garzaya Ingila domin shaida jana’izar Marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth ll. A halin da ake ciki yanzu dai za a iya cewa babu jagora da ke riƙe da ragamar shugabancin Najeriya kasancewar Shugaban da…

Cigaba Da Karantawa